Labaran Duniya

Gwamnan kaduna El Rufa’i Ya Sakeyin Rusau

Mazauna unguwar Malali sun wayi garin Lahadi cikin ɓaraguzan rukunin gidaje da ke Malali Low-Cost sakamakon rusau da gwamnatin Jihar Kaduna ta yi. 

Bayanan da BBC Hausa ta tattara sun nuna cewa da misalin ƙarfe 11:30 na daren Asabar ne jami’an tsaro suka isa unguwar da ke ƙwaryar birnin Kaduna, inda suka fara rushe gine-ginen. 

Wani mazaunin unguwar mai suna Titus Katuka ya ce tun shekarar 1976 suke haya a gidajen waɗanda mallakar gwamnatin jihar ne amma a 2017 gwamnatin Nasir El-Rufai ta ce za ta sayar musu da su. 

Ya ce lokaci guda kuma gwamnatin ta ce za ta rushe su domin gina kasuwa a wurin bayan ta mayar wa da waɗanda suka fara biya kuɗaɗensu, abin da ya sa suka kai ƙara kotu. 

“Ni ba a zo kan layinmu ba amma ban sani ba gobe ko jibi za su iya ƙarasowa,” in ji shi. 

An gina rukunin gidajen na Malali Low-Cost ne domin masu ƙaramin ƙarfi.

Rushe-rushen na daren jiya Asabar sun shafi rukunin gidaje ne da ke kan layukan Gambia da Siera Leon na unguwar. 

Kazalika mutanen sun ce jami’an tsaro sun harba musu hayaƙi mai sa hawaye kafin fara aikin rusau ɗin. 

Wasu hotuna da aka yaɗa a shafukan sada zumunta sun nuna ɓaraguzan gidajen da aka rusa. 

A ‘yan shekarun nan gwamnatin Kaduna ƙarƙashin jagorancin Nasir El-Rufai na rusa wurare da ta ce an gina su ba bisa ƙa’ida ba, ciki har daa kasuwanni.

—- kuci gaba da bibiyar shafin ArewaTrending.com domin samun ingantattun labaran duniya cikin sauki —-

Leave a Reply