Littafan Soyayya

Madubi Sha Kallo – kashi Na 1 (( Littafin Hausa Na Soyayya ))

1

Iska ce me tafiya kunshe da kamshin ruwa Ke kadawa a saman tsaunin, kana iya jin rangajin rassan bishiyoyin dake cunkushe da gurin. A daure da jikin wata bishiyar dorawa, wata matashiyar budurwa ce hannuwanta a daure a guri daya, fuskarta a rufe da bakin kyalle, iskar yammacin tana barbaza gashin kanta dake bude tsirara, hankalinta a tashe sai shure-shuren kafa take. Matashin dake tsaye a gabanta da takobi a rike a hannunsa ya kalle ta tare da bushewa da dariyar mugunta. “Yarinya dama ki daina wahalshe da kanki kina ta shure-shure tunda hakan ba zai hana miki mutuwa ba.” “Hafizu!” Kamar daga sama yaji an kira sunansa a dai-dai lokacin da ya hade hannunsa guri guda ya daga takobin da nufin raba kan budurwar da gangar jikinta, takobin ta subuce daga hannunsa ta fado kasa, kyangyaran! Ya tsuke fuska, jikinsa yana 6ari tare da razani ya waiga bayansa bai ga kowa ba, ya waiga dama-hagu ya leka gabansa ba kowa, haka ne yasa ya hakikance eewa kunnuwansa ne ke zolayarsa. Ya sunkuya da nufin dauko takobinsa dake yashe a kasa tana daukar ido tamkar goshin sabon Kwastsam!, ba zato yaji saukar wani busasshen abu a kafadarsa kamar hannun kwarangwal. Yayi mutuwar tsaye, razani da firgicin da suka bakunce shi suka sa ya sau baki tamkar ya fashe da kuka. Yana makyarkyata tamkar wanda aka watsawa Ruwan sanyi A lokacin Jaura

2

A hankali ya juya yayi tozali da motsattsen matashin dake tsaye a bayansa yana murmushi dai-dai da yamusasshiyar fuskarsa. Hafizu, yayi ajiyar zuciya tare da lumshe ido. A yanzu ya samu nutsuwa saboda tabbacin da ya samu daga zuciyarsa cewa wannan motsattsen matashin dake gabansa amincin dake tsakaninsu zai sa ya rufa masa asiri yayin aikata duk wani abun ki ko da kuwa ace ubansa zai shanshanawa kamshin mutuwa. “Gwaska, ka fara bugun kasa ne?” Hafizu yace yana mai mamakin ganinsa a inda bai yi zato ba, “Sa’ar dake biye dani ce ta nuna mini inda kake.” “Kamar yaya?” Hafizu ya tambaya, idonsa a kan Gwaska. “Kamar yadda nazo na taya ka aikin da kake shirin aikatawa yanzu.” %D “Kisan kan?” “Baka bukatar mataimaki ne?” Ya fada tare da dafa kafadar Hafizu da ana iya ganc sanyin jikinsa daga fuskarsa, kalaman abokin nasa sun dasa masa rudanin tunani ba tare da ya shiryawa hakan ba. “Kana magana da kurman lafazi, da zaka warware mini zare da abawa da na fahimce ka.” Gwaska ya manne idonsa na hagu tare da kallon Hafizu a kaikaice. “Hafizu ba kai kadai ne kake jiran zuwan irin wannan ranar ba, har dani. Tun da dadewa nake bibiyar rayuwar Hadiza saboda na samu kadaicin da zai bani

3

damar daukar fansar bakin laifin da ta aikata mini.’ Rudanin daya bakunce shi ya sake shi, mamaki ya maye gurbinsa. “Wanne bakin laifi ta aikata maka Gwaska?” Gwaska yayi murmushi tare da ajiyar zuciya, ya girgiza kansa cike da takaici. “Wata rana muna rubuta jarabawa sai biro na va tsaya cak. A kusa dani Hadiza ce, na tambayeta ta bani aron biro amma sai ta harare ni, ni Gwaska tare da cewa bata ba dan iska aron kayanta. Tun daga wannan lokaci na rike ta a raina ina jiran zuwan ranar da zata zo na nuna mata cewa ni dan iskan ne na a buga a jarida kamar yadda tace, ba kuskuren baki tayi ba. Na jima ina bibiyar rayuwarta. Ranar bata zo ba sai yau.” Hafizu ya girgiza kai tare da mamakin yadda Gwaska mai bakin hali ya yanke wa Hadiza hukuncin kisa daga kawai ta hana shi aron biro. “Na sani tun da dadewa baka yafiya, kuma baka mantuwa sai ta abu biyu, karatu da alkhairi, ba shakka. Hadiza ta cancanci kisan kai tunda har tayi gangancin hana ka aron biro.” Gwaska bai ce komai ba ya sha gaban Hafizu, ya dyrkusa ya dauki takobin dake yashe a kasa dab da yatsun kafarsa, ya mike. A lokacin da ya ďaga takobin sai Hafizu ya dakatam dashi da cewa “Gwaska dakata, ina ga Hadiza ta hutashshe mu. Fuskarsa a ďaure ya waigo suka hada ido da Hafizu “Da tayi me?”

4

“Da ta mutu mana tun kafin kayi gunduwa-gunduwa da namanta, Gwaska ya juya ya kalli Hadiza, a yanzu da take a daure ta sandare kamar kifin gwangwani, ta daina shure- shure ta bar hargagi. A hankali ba tare da wata fargaba ba ya fara takawa har vu isa inda take, ya dora hannunsa a gcfen wuyanta dab da mukamukinta bai ji motsin bugawar jini a babbar jijiyarta ba, ya kara kunnensa dab da kirjinta, shiru ba bugawar zuciya. Ya kama hannunta ya daga sa’an nan ya saki, ya koma ya bugi gangar jikinta sharaf kamar an saki hannnun mai cutar shan inna, idanuwanta sun canza launi sun koma farare, Gwaska ya juyo suka hada ido da Hafizu. a lokaci guda suka bushe da dariya, wacce amonta ya hadu da sautin rangajin bishiyoyin da na iskar yammaci yayi amsa kuwa a saman tsaunin. “Hadiza ta mutu ta huta.” Suka fada a tare. COLLEGE OF EDUCATION GUMEL. Dalibai maza da mata na ta zirga-zirga a gaban dakin daukar darasin, wasu kuma a zazzaune a kan bencinan dake kafe a karkashin bishiyoyi wadanda an tanade su ne musamman saboda hakan. A gefe guda dab da kofar shiga dakin daukar darasin, wani matashi ne sanye da kananun kaya na manyan yara, yana bawunsin yana tsalle tare da jejjefa hannu tamkar mai shirin rera wakar gambarar turawa. A gefe dashi wata matashiyar

5

budurwa ce rungume da littattafanta yana Isara ta, ita kuma tana ta washe baki cike da jin dadi kamar an bata kwangilar tallar makilin. “Kin san ko? Da za’a tsaga jikina sai an ga kalar jininki a cikin nawa saboda son da nake miki Shahuda. Ta kyalkyale da dariya. “Na gode Hafizu dan sanata.” Ya motsa kafada. “Kin ga fa ke kyan ki daban ne, takunki daban ne, kwalliyarki daban ee, komai naki daban ne da na sauran mata, don haka ko a zuciyata ke…” Hafizu bai karasa ba saboda tozalin da idonsa yayi da wata farar tauraruwar budurwa wacce tazo ta gifta ta gabansu tana karairaya ta shiga dakin daukar darasin, ta shige tare da nutsuwa da hankalinsa, a ransa ya saka cewa ya zame masa dole ya bita ya amshi kayansa. Tana shiga cikin dakin daukar karatun sai ya fura takuwa çike da iyawa yana jejjefa hannu da nufin bin ta. Shahuda ta bi shi da kallo cike da takaici. “Hafizuu !… Hafizu !!” Ta kira shi. Ya share ta tamkur bai ji ta ba. Ta dafe kanta cike da damuwa. Ta ja gwauron numfashi sa’an nan ta lumshe ido. “Oh shiit! Na hudu da sharrin Hafizu Dan Sanata.” Hafizu ya shiga cikin dakin daukar karatun yana leke-leke, can ya hango ta a kurshen dakin a tsakanin wasu kujeru, da littattafa a kan teburin dake gabanta. Yayi murmushi sa’an nan ya fara takawa cike da iyawa da nufin isa Gareta.

6

Sa’ar da yaje Gareta sai yayi murmushi. bai damu ya mata sallama ba sai kawai ya dan durkusa ya rage Isawonsa tare da zuba mata ido yana mata kallonsa firgita ‘yam mata. “‘Y’am mata sannu ko.”. Ta daga kai ta kalle shi. kwarjini da cikar halittarsa suka fizge ta zuwa ga yin kasalallen murmushi. “Yauwa sannu dai ‘Yan samari,”. “A lokacin da na ganki sai naji wani daddadan kamshi ya bugi hancina, na biki da kallo lokacin da kika durkusa kika tattara PAPU muhimmaci. kika shigo dasu nan, na biyo ki ne na karbi abi na. Ta ja gwauron numfashi tare da dafe kirji. “Ni?” Ta nuna kanta. ta ci gaba “Kai Malam ba ni bace, ko dai ka samu rudewar tunani ne?” “Kin ga nayi kama da tsoffī ne?” “To koma dai mene ne ni ban ma kula da wani mutum ba a lokacin da zan shigo nan ballantana na ci karo da wani abu nasa a kasa. Kaje ka nemi wanda ya dauka maka abunka bani ba.” Ya murmusa tare da sakin fuska. “Yanzu zaki ce ba kece.kika dauke zuciyata, hankali da nutsuwata kika shigo dlasu nan ba? Na biyo ki ne na karbi abi na. Ta bushe da dariya. “Ka cika abun dariya.” “Ke kuma gashi kina fada da gaskiya.” Tayi murmushi. “Yanzu dai me kake so kace?)”

7

Ya dan lumshe ido ya kalleta a cikin salon yaudara “So nake nace Allah ya miki baiwar kyau, cikar halitta, kamala da nutsuwa. Ta kyalkyale da dariya cike da jin dadi. Hafizu ya ci gaba Sunana Hafizu Dan sanata ina zaune tare d. Mahaifina Sanata Mujaddadi Nasidi a Abuja cikin as Ta daga kai da sauri tare da zuba masa ido. “Na dade ina jin labarinka a wajen kawayena, dam. kai ne Dan sanata?” Yayi murmushin jin dadi tare dla zakuda kafada. “Eh nine. Me zaki ce in nace ina sonki?” Ta lumshe ido tare da jin dadi “Babu bukatar nayi shawara da ko da zuciyata ne aminta da kai. Yi farinciki da murna kafin na kwantankwacin ni saboda ina sonka, fatana da rokona a gareka shine ka rike ni amana. ka zama masovin mutu ka-raba, masoyin rabuwa-babu dla sanyi ko zafi ku wann canjin rayuwa. Sunana Zahra’u. Ya dan yi tsalle kamar wanda ke murnar zura kwallo a raga yayin gasar wasan kwallon kafa. va kaiwa iska duka cike da farinciki. “Na miki alkawarin…” 09 Bai karasa maganar ba saboda tozalin da yayi da wata dakwalwar budurwa a waje ta tagar dakin… Ya hango ta tana tafiya mai fizgar h.akali, ya sau baki ya bita da kallo. Ya fara tafiya a haakali, idonsa tar a kanta. Zahra’u ta bishi da kallo cike da mamaki. “Hafizu ina kuma zaka?”

8

Ba tare da ya juyo ya kalleta ba ya daga mata hannu vana mai mata nuni da kar ta dame shi, ya ci gaba da tafiya har ya fita a cikin ajin. HAFIZU Kyakkyawan matashi ne, dogo ma’abocin iya dressing da kwalisa, daya daga cikin daliban da zasu kammala karatunsu a watan Ogusta na shekara mai zuwa a kwalejin ilimi ta garin Gumel dake jihar Jigawa, a cikin makarantar duk wanda ya rantse da cewa ba sama da Hafizu a wajen kula ‘yam mata ba shakka bai yi karya ba. Rahoton dalibai y’an sa’ido, bin diddigi da gaza gani sun tabbatar da cewa a kalla a rana Hafizu ya kan tsaya da mata sama da goma sha biyar, in dai Mace fara ce ko zata daga hannu ta kwada masa mari in ya mata magana, sai yayı. A gare shi ba abun bakinciki kamar farar mace ta wuce ba tare da yaga fuskarta ba, in haka ta faru nan da nan zazzabi da ciwon kai zasu rufe shi har sai ya sha magani ko kuma wata farar budurwar daban tazo ta wuce yayi tozali da fuskarta sa’an nan ya samu sauki. Yana da ruwan ido ta yadda yanzu-yanzu zai hadu da mace su zauna suyi hira da dararraku, yayi mata alkawarin shi da ita mutu-ka-raba, amma da zarar ya kyalla ido yaga wata farar tauraruwar shikenan ya manta da alkawarin da ya yiwa wata a baya. Habiba, Zulaihat, da kuma Maijidda, sune kadai yam ‘matan da soyayyarsu da Hafizu ta dan yi nisan kwana na adadin awanni arba’in da hudu kacal! kafin

9

daga bisani su da kowa ya kama gabansa daga bisani su rabu da tsiya-tsiya kowa ya kama gabans suyi rabuwar Allah hada kowa da rabonsa. Wata rane abokansa suka titsiye shi da tambayar dalilin rabuwarsa da wadannan dakwalen ‘yam mata, sai ya kada baki ya ce “Habiba, wani kaimi ne a kafarta… Tsorata ni yake Madubi wallahi”. Wani a cikinsu ya ce “Duk da baka san da kaimin nata ba sai yanzu? To mun ji… Zulaihat da Maijidda fa me ya raba ku?” Hafizu ya yi murmushi. “Zulaihat ta fiye kauyenci, kullum sai ta sako wani hijabi burum-burum kamar wata tsohuwa kamar cus, ita kuma Maijidda kalar fatarta ta dan sirka da baki… Bana son bakar mace a banza ta haifa mini munanan ‘ya’ya.” 16 Suturu na alfarma, na gani na fada da Hafizu yake sanyawa sun isa su tafi da hankalin duk wata macen da ya tsaya da ita, sai ya karkace kai yace “Ni dan sanata ne, ina zaune ni da mahaifaina da sauran y’an uwana a Abuja a Aso rock, na fado makarantar nan ne accidently saboda ba da ita nafi cancanta ba. Abbana nc yace yafi so na zo na zauna a cikin ‘ya’yan talakawa nayi karaiu caboda suma mutanc ne kamar kowa.” Dole su yarda saboda sunan mahaifinsa iri daya ne da na sanatan jigawa ta gavas, baya da haka kuma

10

suturarsa da cikar halittarsa kaďai sun isa su gigita duniyar tunanin duk wacce ya tsaya da ita. Ina ma ace ‘yam matan da Hafizu yake gigita nutsuwarsu da sutura da karyarsa sun san asalinsa, da basu saurareshi ba. Abun da ‘yam matan tare da sauran dalibai, basu sani ba shine, Hafizu dan talaka ne gaba da baya, : talakan kauye. Talakan da sai ya fito da hatsi a rumbu an casa masa kana ya dauka ya kai kasuwa ya sayar sa’an nan ya samu kudin kayan miya da sauran bukatun rayuwa, abun da ‘yam matan da sauran dalibai ba su sani ba shine Hafizu dan kauyen kayau ne domin a shckara sai an ci gagarumar sa’a mota ko babur su shiga garinsu sau daya tal, sai dai ai ko ba komai suna da motar kauye… Shi ma ya iya tuka ta, amalanke kenan! Mujaddadi Nasidi shine mahaifin Hafizu yana daya daga cikin daidaikun mutanen dake da akidar ‘ya’yansu sai sun yi karatun boko a Garin Baba Modu, a baya yana ji yana gani Mahaifansa suke boye shi a cikin rumbu ko kuma a randar ruwa saboda kawai sun kulla gabar sai baba ta gani da karatun boko, ɖa zamani yayi nisa sai yaga wadanda suke zuwa makarantar saboda rashin gatanci a baya a yanzu sune sanye da sutura mai kyau, sune da muhalli mai kyau, abinci mai kyau, jikinsu bul- bul saboda gwamnati ta dauke su aiki tana biyansu kudi duk wata, su kuma da aka yi musu abun da ake ganin shine gata a da can baya gasu nan jiya i yau, suje gona su dawo su sha farau-farau ko tuwon tsaba da miya kar ta kafura. Hafizu yana samun makudan kudin da yake fantamawa dasu ne tare da sayen suturu masu tsada ta

11

hanyar karerayi da yake zuwa ya yiwa mahaifinsa a duk lokacin da yaji aljihunsa ya fada. Ya kan ce dashi, “Baba an ce mu kai kudin joga-joga, agriculture brighter grammer.” Ba dan yasa a ransa cewa ko zai zauna bashi da ko asi sai Hafizu yayi karatun nan ba da tuni yayi watsi da lamuransa saboda yawan bukatunsa, da zarar ya ganshi yazo gida sai gabanshi ya fadi saboda ganin Hafizu dai- dai yake da damin gero goma sha bakwai ko turkakken rago Idan Hafizu yazo zai tafi bayan ya bashi kudin ya kance dashi, “Don Allah Hafizu tun da dai ga kudin nan na sayar da hatsina na baka, ka taimaka kada ka dawo garin nan kwana kusa, ka taimakawa rumbun hatsina.” Hafizu ya kan yi murmushi yace, “Kada ka damu Baba, da yardar Allah ba zan dawo ba sai kun hada noman hatsi.” Mujaddadi Nasidi sai yayi murmushi ya dafa kafadar hafizu. %3D “Kaga ja’iri, wato yanzu boko ta sangartar da kai ka fara gudun noma ko? Allah dai ya taimaka. Ka mai da hankali a kan abun da ya raba ka damu ya kai ka can, ka sani cewa komai kake nema a sabanin abun ake samunsa, sai an sha wuya ake jin dadi, sai anyi bauta ake samun yanci. Idan kayi kuka da safe sai kayi dariya da yamma, Hafiz!” Hafizu yana da abokai na garari a cikin gari, ‘ya’yan masu kumbar susa masu hannu da shuni da suka shaku

12

da juna tamkar abokan kuruciya, a wajensu yake samun ron motocin da yake shigowa dasu cikin makarantar lokaci-lokaci yana toroko, hura hanci da baza fadi. Musamman yasa aka buga masa lambar mota ta bogi HafizuO01 har zuwa O10, a duk lokacin da ya samu aron mota sai ya cire lambarta ya mayc gurbinta da tasa. Da farko Hafizu a cikin makarantar yake kwana kafin daga bisani ya kulla abota da Bala Gwaska su koma cikin gari su kama daki. Gwaska shi ma kamar Hafizu dan talaka ne gaba da baya sai shegiyar karya kamar guntun yaki, yana kokarin ganin ya lalata duk wacce ya samu fuska daga gare ta. Wata rana, Gwaska da Hafizu sun je hira wajen wata yarinyarsu Farida wacce a dakin kwanan dalibai mata wanda yake a makarantar (female hostel), su ka zauna a kan benci a gefe guda sa’an nan suka kira ta a waya, ta fito. Ta zauna a kusa dasu suna hira kafin daga bisani ta tashi ta koma cikin dakin kwanansu ta fito da ma’adanin zafin abinci food flask ta mikawa Hafizu. Ya karba ya bude tare da kallon abun da ya kunsa a yatsine, ya daga kai ya kalleta. “Farida mene ne wannan. Tayi murmushi, ta fara magana cike da jin dadi. “Taliya ce jiya da daddare na dafa ta da yawa, ragowarta ce na dumama yanzu na kawo muku.” Gwaska ya fara salallami, Hafizu yayi kutubol da flask din sa’an nan ya fashe da kuka. “Wannan shine tozarci mafi girma da wani mahaluki

13

ya taba yi mini, ni dan sanata Mujaddadi. Farida, ambaci dumame a gabana sa’an nan har kina fassara ni de mutumen da zai ci. Ya fada a cikin muryar kuka. Gwaska ya fara lallashinsa tare da kallon Farida iqnpo wacce ta rikice. “Kin yi ganganci Farida, ai ba’a ambatar a kalla ko da sunan dumame ne a gaban dan sanata, yanzun nan zai fara mashashshara da zazzabi.” Ya juyo ga Hafizu. “Yi hakuri, tashi muje asibiti a kara maka ruwa. Yi hakuri kada ka janyo mata kwanan chaji-ofis. Matukar Sanata dan Nasidi yaji wannan labarin to bar ta ita, har tsoffinta sai sun gwammace kida da karatu. Ya tallafi kafadfar Hafizu ya mike a tsaye yana kuka, Farida ta bisu da kallo tare da mamaki da al’ajabi. “Allah Abun da Hafizu ya fada kenan kafin su bar tafi gidan kwanansu a cikin gari su jika gari da suga su 11 isa Farida, kin cuce ni. ns uuns tsama su ci. Duk da iya shegen Hafizu, wani abu game dashi shine ba wanda zai ce ya taba ganinsa da littafi yayin daukar darasi ko yin bita amma da zarar an yi jarabawa shine mutum na farko a cikin jerin zakarun da suke nasara. Akwai lokacin da wani Malami ya shigo dakin daukar karatunsu don gabatar da darasi, kafin ya fara gabatar da darasin ranar sai ya fara da yi musu tambaya a kan darasin jiya. A cikinsu aka rasa wanda zai bada

14

amsa, sai rarraba ido suke kamar dillalan kaji. Ga mamakin daliban da kuma malamin duk da yake Hafizu baya nan aka gabatar da darasin jiya ya tafi sheke ayarsa, sai ya đaga hannunsa. “Yes Hafizu Mujaddadi Nasidi.” Malamin ya bashi izinin bada amsar. Hafizu har malamin sai da ya sau baki yana kallonsa saboda yaji har abun da ya rage bai fada ba a lakcar sai da ya zazzage shi ciki har da na lakcar ranar. Wani abun ma da ya fada Malamin bai ma sanshi ba. Bayan da Hafizu ya hada bayaninsa, gaba daya ajin ya rude da tafi da sowar dalibai tamkar a ranar karshe ta kammala jarabawar tashi ya fara zazzaga jawabi, ba daliban ba 12 daliban sakandire. Dogon Malamin tsololo mai kamar iska ta dauke shi bayan yayi ajiyar zuciya tare da ba dalibai umarnin su tsagaita da hayaniyar da suke haka nan, sai ya kai dubansa zuwa kan Hafizu dake can a karshen dakin, yace “Hafizu naga baka nan na gabatar da lakcar jiya, kuma bana jin a cikin daliban nan za’a samu wanda zai maka bayani kwatankwacin yadda kayi a yauzu, mene ne sirrin? Jikan Nasidi.” Hafizu ya murmusa. “Nonon Gyatumata.” “Ban gane ba ‘’ Ya fada tattare da yanayin rashin fahimtar inda Hafizu ya dosa. “Ina nufin a nonon gyatumata na zuki boko tun ina Yaro. Gaba daya daliban suka bushe da dariya, wasu kuma

15

suka juyo da hankalinsu da kuma kallonsu suna masu mamakin yadda ya zuki boko a non gyatumarsa. Wasu kuma shewa kawai suke suna cewa “Sai kwaro.” Kaifin basirar Hafizu yasa dalibai kan zo su same shi su ce, “Dan sanata idan ka samu lokaci zan zo muyi darasi na musamman, extra lesson.” Idan namiji ne ya fada masa haka ya kan ce dashi bashi da lokaci, idan kuma yaga mace ce, a matan ma fara sai yace “Ina da lokaci amma sai karfe goman dare.” Idan ya hadu da ‘yar duniya irinsa ta kan ce dashi, “A ina zamu hadu?” Shi kuma sai yace. “Mu hadu a bayan (Laboratory).” Sai ta masa godiya ta tafi bisa alkawarin zasu hadu a wajen in lokacin yayi. Shi kuma sai ya bita da kallo tare da cewa 04 “Wai, garin dadi ba kusa ba! Allah ya kai mu dare na kwashi danasha.” Akwai ranar da wani Ustaz á ajinsu ya taba samun Hafizu da Gwaska yana musu nasiha a kan illar abun da suke. “Ya kamata acc rayuwarku ta dau sabon salo, rayuwar da kuke ciki a yanzu ba rayuwa ce mai kyau ba, bakar rayuwa ce da munin aikin da kuke aikatawa komai daren dadewa sai hotonsa ya bayyana a kan ahalinku. Shin ba kwa tunanin ranar da za’a tambaye ku yadda

16

kuka gudanar da rayuwarku ? Ba kwa tunanin ranar da za’a tambaye ku yadda kuka gabatar da samartakarku ? Ba kwa tunanin akwai mala’iku tare daku da suke rubuta ayyukanku ? Da ma ace kuna tuna cewa wata rana za’a wayi gari baku , in kuka mutu wacce gudunmawa kuka ba addininku da zala tuna ku ? ” Suka kalle shi a kufule tare da girgiza kai . ” Gaka a haka kamar wayayye ashe kallon kitse muke yiwa rogo . Cewar Hafizu . Gwaska ya nuna shi da hannu yana cewa ” Dube shi da Allah yazo ya samu a gaba yana yi mana fada kamar ya samu ‘ ya’yansa . ” Ustaz yayi murmushi . ” Ba fada nake yi muku ba , nauyin da ya rataya a kan duk wani musulmi na kawar da abun ki da hannu ko baki nake saukewa . In ma baku sani ba ku sani Allah baya yafe hakkin ‘ wanda aka zalunta , alkawarinsa tabbatacce ne baya canzawa , duk abun da mutum ya shuka shi zai girba . Ko ku daina ko ků ci gaba ba ruwana . Akwai ranar kuka tana zuwa , rañar nadama , ranar da hoton cutar da kuke wa ‘ ya’yan mutane za ta bayyana a jikin jininku . ‘ Ustaz yače sa’an nan ya tashi ya fita ya barsu , suka kalli juna suka fashe da dariya tare da ta fa hannu cikin shakiyanci . ” Kawai daga mutum ya bushi iska sai ya bar gashi ba ya – ba ya a fuskarsa shi ba gwaggon biri ba wai nan shi Ustaz . “

17

La’asar ce sakaliya , a wani kebantaccen waje mai yalwar bishiyoyi dake samar da ni’imantacciyar iska wa mahalukin dake zaune a karkashinsu , a zaune a kan daya daga cikin bencinan da suka zagaye wajen , Hafizu ne ! Ya dora kafarsa ta dama bisa ta hagu kamar wani dan minista , in ka dauke bakar hula hana sallah facingcup da ya aza bisa kansa to komai na jikinsa fari ne , farar riga t shirt , farin wando jeans , farin takalmi a zunguri duniya , a rike a hannunsa na dama wata waya ce samfurin nokia Lumia520 . ya sunkui da kansa yana kallon fuskarta , ya tattara hankalinsa gaba daya kan tadin da yake da wata sabuwar buduwarsa a dandalin 2go.si sta Amon takun tafiyar da ya bakunci kunnuwansa kwas – kwas yasa ya daga kansa ya kai kallonsa inda yake tsammanin daga nan ne sautin yake fitowa . Daga nesa ya hango ta ta nufo inda yake , suka hada ido kana yayi murmushi , murmushin Allah ya kai damo ga harawa kana a lokaci guda ya cije baki . ish Matashiyar budurwar ta ci gaba da tafiya a hankali kamar mai tausayin kasa , sanye take da atamfa holland ruwan goro . y’ar fingil – gilar rigar da ta manne a jikinta ba abun da ta rufe wajen bayyanar da kyakkyawar halittarta ta cikakkiyar budurva . Fararen idonta na sakaye cikin wani bakin tabarau ba mutunci ( no respect ) . daddadar iskar la’asariyar dake kadawa ta taka rawa wajen kada yalwataccen gashin kanta mai santsi da kyalli akan gadon bayanta , dan siririn gyalen da ta yaſa

18

bisa kafadarta akwai ya babu ne tunda bai hana jama’a tozali da abubuwan da bayyanarsu yake wanzar da bala’i da zina a bayan kasa ba . Jan takalmi cicciba ni na hau jaka wanda ke fitar da sauti kwas – kwas shike isar da sakon wucewarta ga mutanen dake zaune jefi – jcfi a kan hanyarta ta zuwa wajen Hafizu dan sanata , wasu suyi Allah wadai tare da tofin Allah tsine wa bakin direshin da tayi da sunan wayewa , wasu kuma su yi mata fatan shiriya , yayin da mafiya yawa suke zuba mata ido suna hadidiyar yawu , suna kallon gaba da bayanta tare da kyasa kyakyawar halittarta a zuciyarsu . ” Dije ! Dije ! ” Hafizu ya faca sa’ar da ta karaso gareshi sa’an nan ya bita da kallo daga kasa zuwa sama . ” Hadiza , kin hadu fa ! Irin wannan kwalliya haka ? ” Tayi murmushi kana a lokaci guda la fara kokarin zama akan bencin kirjinta kankame da wasu liitattafa . ” Na gode Hafizu da yabon kwalliyata , sai dai kuma ban san me zaka ce ba idan nace saboda kai na kure adaka . ” Ta zuba masa kyawawan idonta tana jiran martaninsa . ” Ni kuma ? ” Ya fada tare da mamaki . D ” Kai mana , in mamaki kake ka daina saboda kana da babban matsayi a wajena , zuciyata ta dađe da narkewa a kan sonka , idaniyata ta makanta ga barin kallon fuskar kowa sai taka . Tuntuni nake jiran zuwan ranar da zata zo

19

na tona asirin zuciyata game da kai , ranar ce bata zo ba sai yau . ” Ya bita da kallo tare da gamsuwa da kyanta , a zuciyarsa yana mai jinjina kyakkyawar halittarta , a ‘ yam matan da yayi barkatai ba mai kyawunta , a cikar halitta ba kamarta , a taushi da dadin murya kamar ana busa sarewa ba irinta , tabbas yau katon kifi ne ya faço cikin komarsa . ” Na riga ki a zuci kin riga ni a baki , idan nace haka to ina nufin zuciyata tuntuni ta aminta da ke , tuntuni ta yaba da kyau da nutsuwarki . Kawai dai kin riga ni furtawa nc Ta kalle shi cike da jin dadi tare da kyalkyalewa da dariyar farin ciki . ” Yau farin cikina zai yadu , kuncin zuciya zai tafi , gani ga Dan sanata Madubin fuskata yana shelanta mini cewa ya amshi soyayyata . ‘ Kamshin turaren jikinta ya cakuda da numfashin da Hafizu ya shaka ya shiga cikin hancinsa ya samar masa da wani yanayi mai sa nishadi da annasluwa , ya dan lumshe idonsa kana yace ” Duk yadda zaki fassara farin cikinki baki kai ni ba . Da a Kano muke da na hau dutsen Dala na shelantawa duniya cewa yau Hadiza ta zama tawa . Ya kalli littattafan dake kan cinyarta . ” Da wanne course zamu fara extra lesson din . ” Ta kalle shi tare da yin walainiya da ido . ” Mhm , ina ga sai mu fara da ( Micro – biology ) . Amma ina ga dą zamu shiga cikin ajin can da zai fi . ” Ta nuna ajin dake gabansu da yatsanta .

20

” Ba damuwa , muna iya zuwa can din ” . Hafizu ya fada kana suka mike a lokaci guda suka fara tafiya a jere lokaci – lokaci kafadunsu na bugun juna . Suka tafi zuwa wani aji mai yalwar duhu da rashin jama’a inda Hafizu zai yiwa Hadiza extra lesson , suka ci gaba da tafiya suna hira da dararraku . Suka shiga cikin ajin daga shi sai ita , suka zauna akan kujera daya ta yadda kwankwasonsu yana shafar na juna yayin da littattafan Hadiza suke zube a kan teburin da ke gabansu . Saurayi Hafizu ya fara yiwa Hadiza bayani ta hanyar yin amfani da hasken cocilan din dake makale da wayarsa , sai dai abun da dan saurayin tare da matashiyar budurwar basu sani ba shine , basu kadai ne a cikin ajin ba , su uku ne . Shaidan ne cikon na ukunsu , shi ya kawata musu sha’awar juna har suka ji zukatansu na umartarsu da su biyawa juna bukatarsu . Hafizu ne ya fara kamo hannun Hadiza yana murza shi , ba tare da bata lokaci ba suka biyewa son zuciyarsu tare da kururuwar da shaidan yake musu wajen kawarwa da juna sha’awa … Suka aikata kazamin laifin da Allah ya hana mu kusantarsa , zina . HADIZA A da can ba haka rayuwarta take ba ! Tana rayuwa ne tare da mahaifinta Alhaji Lukman hamshakin attajiri a garin Biriwa tare da Mahaifiyata hajiya Zuwaira da kannenta biyu mata Nabila da Bara’atu . Da can can kafin zuwan Hadiza kwaleji yarinya ce mai kamun kai , kunya da alkunya , ma’abociyar sanya sutura ta mutunci da kamala .

21

A lokacin da take dab da kammala karatun sakandirenta wani saurayi mai suna Shamsu ya kutso cikin rayuwarta ya koya mata sonsa , dan hutu ne gaba da baya , gwani ne wajen saka zararrukan soyayyar dake sace zuciyar mace . A haka Hadiza ta samu ta kammala karatunta na sakandire suna tafka soyayya ba ji ba gani wai auren kurma da makaho ita da Shamsu , a haka suka yi matukar shakuwa , shakuwar da ta sa suke ganin baza su iya rayuwa ba tare da junansu ba , shakuwar da tasa suke ganin sun zama tamkar hanta da jini , ruwa da iska ko wani sauyi na rayuwa ba zai girgiza soyayyarsu ba , a haka suka sawa juna zoben alkawari tare da yiwa juna alkawarin aure a tsakaninsu . A lokacin da Hadiza take kokarin gabatar da shamsu ga Mahaifanta a matsayin zabinta , a lokacin jarabawarta ta kammala sakandire ta fito , amma duk da haka bata yi kasa a gwuiwa ba sai ta sanar da Mahaifiyarta cewa ta isar da sako ga Abbanta cewa zata kawo Masoyinta Shamsu ya gaishe su . Hajiya Zuwaira ta isar da sakon Hadiza , da safon ya ishe shi sai ya kira ta falonsa ya fara da cewa ” Hadiza na samu sakonki daga bakin mahaifiyarki , sai dai kiyi hakuri don kuwa abun da zai fito a bakina ya saba da tsarinki , ba dai – dai bane da son zuciyarki . Abun ne 1 da nake so na faţa miki shine daga yau , daga rana irin ta yau ki fadawa Shamsu , mutumen da kike ikirarin cewa shi masoyinki ne kada na sake ganinsa a kofar gidan nan . Ta razana tare da yin nannauyar ajiyar zuciya , a lokaci guda ta dafe Kirjinta . Ya yake ambaton rabuwarta

22

da Shamsu ? Shamsu abun yabonta a mafarki ko a farke . Alhaji Lukman ya kalleta ba tare da ya damu da yanayin da ya bakunceta ba ya ci gaba da jawabinsa . ” Eh , na yanke wannan shawarar ne ba don bana son farincikinki ba sai don na cika wani ajiyayyen burin da yake raina , burin bawa ‘ ya’yana maza da mata damar samun yin karatun boko mai zurfi . Hadiza ta fara kuka . Ya kalleta tare da yin kasalallen murmushi sa’an nan ya ci gaba ” Kina jina ko Hadiza ? Na gama shirya komai , na gama tsara komai , karatu zaki tafi Kwalejin ilimi dake Gumel . ” Da Hadiza taji haka sai ta tashi tana gurshekan kuka tana sarsarfa kamar za ta kifa ta shige dakinta . Alhaji Lukman ya hada ido da Hajiya Zuwaira wacce tayi ajiyar zuciya . ” Wai yarinyar nan mai take nufi ne ? ” Hajiya Zuwaira ta tabe baki . ” Tana nufin aure take so mana Alhaji . ” Yayi kasalallen murmushi . ” Aure ai da sauran lokaci tukuna , kwata – kwata ma nawa take da zata so aure yanzu ? Ta bari sai taga karshen boko tukuna sa’an nan ta fara maganar aure . ” ” In bata ga karshen boko ba ai ta zama kisan boko . ” Daga lokacin da Hadiza taji kalaman Mahaifinta tayi kuka kamar ranta zai fita saboda hakan yana nufin rabuwarta da Shamsu ranta , Shamsu wanda ta dau amanar zuciyarta ta đamka masa , wanda ta shiryawa yin rayuwa mai dadi tare dashi . Dole tayi kuka zata rabu da Shamsu dan soyayya .

23

Hadiza tana kwance tana kuka , mamanta ta shigo ta same ta . Ta zauna a gefen gadon kusa da ita , ta shafa kanta cike da tausayawa . Hadiza ta dago da kanta ta kalleta da idonta da suka canza launi zuwa ja . ” Hadiza ki daina kuka tunda kukanki ba zai sa Mahaifinki ya canza kudirinsa ba , kin san da haka . ” Ta daga kai a cikin gunjin kuka ta kalli Mamanta . ” Na sani Mama amma dai a kalla zai rage mini radadin zuciya , ban san ya zan yi na kwance sakar da Shamsu yayi a zuciyata ba , mun shaku da Shamsu , shakuwar da tasa muke ganin cewa dayanmu ba zai iya rayuwa ba đaya ba , mun yiwa juna alkawarin rayuwa a tare komai sanyi da zafi , duk runtsi duk wuya ba abun da zai raba mu sai kaddara wacce bamu iya tsere mata . Kwatsam sai gashi a lokacin da nake shirin gabatar da shi gareku wannan kaddarar ta shigo cikin rayuwarmu , ban san a yaya zan kalli Shamsu ba , ban san a yaya zai fassara ni ba , ban san me zan ce masa ba . ” Ta fashe da sabon kuka . Mamanta ta janyo ta jikinta ta sa hannunta tana share mata hawaye . ” Kiyi hakuri Hadiza komai mai wucewa ne , me yiwuwa ne Shamsu ya jira ki , in kuma an samu akasin haka to ki sani cewa rahamar Allah yalwa gareta , in kika dogara dashi sai ya baki wanda yafi Shamsu komai ta inda baki yi zato ba . ” Tayi iyakar kokarinta wajen nunawa mahaifinta cewa ita fa aure take so !, amma ya dakikance da gan – gan ya gaza fahimtarta . Ta nuna masa cewa a mata auren daga baya sai taci gaba da karatunta a ďakin mijinta , Alhaji Lukman ya daga kafa ya buga yace sam taura

24

biyu ba ta taunuwa , ba’a hada gudu da susar duwawu . auren nan ta hakura dashi kawai . A karshe dole ta hakura , da ta hakura tavi kuka , kukan da bata taba yin irinsa ba a rayuwarta , tayi bakinciki irin wanda bata taba vin makamancinsa ba , zuciyarta tavi kuna tamkar ta tarwatse saboda radadi , nesanta ta da Shamsu tamkar kusanto mata da ajalinta ne . Hadiza bata boyewa Shamsu komai , don haka da vazo tafada masa halin ha’ula’in da yako shirin kusantarsu . ” Gangancin da nayi a rashin sani shine mallaka miki zuciyata . ashe akwai ranar rabuwarmu kafin cikar wa’adi ? Hadiza sha lelem Shamsu haka kowa ko cewa ashe ba hakan ba ne . Ya tsagaita yana huci tamkar mayuniacin zaki . zuciyarsa tafarfasa take , hawaye bai daina gangarowa kan fuskarsa ba . Ya ci gaba ” Hadiza zan tafi da tsananin kewarki , zan nisanta dake , zan koyawa zuciyata kinki wala Allah ko na manta dake . Va tafi , in da rabon ganawa me viwuwa ne wata rana na dawo gare ki … Sai wata rana Hadiza , da na san da zuwan wannan rana da ban kovawa zuciyata sonki ba . da ban bari sonki ya shiga jinin jikina ya zame mini dafi ba . ” Ya share hawayen dako zubowa bi da bi daga idonsa . Ya kalli Hadiza wacce tun zuwanta ba abun da take sai kuka , ya ci gaba ” Ba zan lallashe ki a kan kada kiyi kuka ba saboda na san shine abun da ba zaki iya ba , abun kawai da ya

25

zame mana tilas shine mu rungumi kaudara . ” Jikinsu vayi sanyi , idanduna sun zub da hawave mai radadi … Zuciva lavi kuna katin daga bi sani Shamsu ya tausashi zucivarta da kalamai masu dadi , kalamai na Karfata gwiwa tare da yi mata fatan alkhairi . Sati uku bayan rabun arta da Shamsu . Hladira la latlara komatsanta ta rabu da garin da la saba rasuwa , ta rabu da Mahai fanta ta tati garin ( und / da sunan karatu . A can , walwala da farinciki suka mata adabu , halin kunci da kuka da yawan tunani suka kusanci dunivarta . Abun da ya zame mata kamar wajibi kullum shinc ta kebe daga jama’a ta samu yanavin kadaici la fauna la rafka tagumi tana huka , tana tunanin Shamsu masovinta . Hata runa . Hadiza ce a faune a kan farar kujerar roba a wani kehantacoen waje cunkusho da bishiavi da yalwar inuwa , da littafi a gabanta ta zuba masa ido , hawaye yana kwaranya daga cikin idonta yana sauka a kan littafin . Tsawon lokaci tana cikin wannan yanayin katin daga bisani wata doguwar budurva mai cikar halitta , kvakkyawar sutura da yanavi ta bakunce ta , ta zuba mata ido cike da tausayawa sa an nan ta rage tsawo la dafa kafadarta ” Bajwar Allah mee ke damunki ? Na fahimci cewa kullum sai kin 70 nan kin zauna ke kadai kina tunane tunane tare da kuka ? Ba kva ganin cewa hakan vai iva shafar duniyar karatunki ” Hadiza ta dago hai ta kalleta a lokaci guda ta sa

26

gefen hannunta lana share hawayenta . ” A yanzu ba abu mafi sanya farin ciki a gare ni sama da abun da zai shafi duniyar karatuna ta kowanne fanni . Idan nace ta kowanne fanni to ina nufin ko da kora ce gaba daya daga makarantar . ” Matashiyar budurwar la lumshe ido tare da yin ajiyar zuciyil . ” Baiwar Allah mo yayi zafi haka ? Mene ne tarihinki ? ” ” Ba na son tuna tarihina . Bana son fadawa kowa , saboda a cikinsa ne a ka rusa farin cikina . ” Matashiyar budurwar ta mike tsaye . ta juyawa Hadiza baya ta fara magana a cikin wata nurýa dauke dir tuna wani abun takaici da ya faru da mamallakiyarta a wani lokaci baya ” Ko baki fada mini komai game dake ba , hasashena ya nuna cewa tarihinki yayi kama da nawa . Kee ba karamar yurinya bace ballantana ace kewar gida ce tasa kika zabarwa kanki wannan rayuwar . Wata kila halin da kiko ciki a yanzu yana da nasaba du tilasta miki rabuwa da masoyinki da aka yi a gida a dalilin karatu . Ba abu mai ciwo kamar rabuwa da masoyi bayan shakuwa . masoyin da sonsa ya zame miki dafi a zuciya . Nima irin haka ce ta faru gare ni a wani shudad en lokaci , nayi iyakar Rokarina don na ganar da mahaifana cewa nafi bukatar aure a wannan lokaci , bayan hakan sai naci gaba da kurutuna a gidan mijina , amma sai suka yi fatali da muradina . Bayan nazo makaranta na hadu da Rawaye kala – kala , yawancinmu tarihinmu iri duya ne , dole muka hadu muka nemarwa kanmu mafita . Don haka kema

27

daga yau kin zama kawata , ki daina damuwa . Kasldara cewa haduwarki dani tamkar gangamin haduwar hadarin da zai zubar ruwan da zai wankć matsalolinki ne . ” Ta tallafi kafadar Hadiza ta mikar da ita a traye , la sa hännunta tana share mata hawaye . ” Sunana Nabila Nabil , ke kuma ya sunanki ? ” Ta tambayi Hadiza . ” Hadiza . ” Nabila ba karamar rawa ta taka ba wajen canza launin rayuwar Hadiza daga fara zuwa baka , tà hada ta da wasu fitsararrun kawayenta , kawayen da suka yi tasiri wajen sauya taswirar rayuwar Hadiza . suka sa tayi fatali da nasihar da mahaifiyarta ta mata a lokacin da aka sa jakukkuna da akwatunta mai taya a cikin mota zata rabu da garinsu ta dawo wani garin daban . A lokacin , mahaifiyarta cewa layi da ita ” Hadiza kada ki manta da cewa ke mace ce , ki rike martaba da mutuncinki , ki kula da addininki gwargwadon iyawarki , kada ki yada kunya da yakanarki domin yin hakan zai sa ki aikata komai ciki har da abun da zai shafi mutunci , kamala da martabarki . Kada ki ba shaidan damar da zai gadar miki da damuwa , ki yi imani da cewa komai kaddara ne . Ki yarda cewa komai ba naki bane , komai ba zai taba kasancowa naki ba , dukkansu abu na wanda Allah ke bayarwa . Komai zai wuce tamkar ba avi ba … Wata rana sai labari . ” Wata kila da acc maliaifanta sun mata aure tun a lokacin da ta bukata , da duk haka bata faru gare ta ba … Wata kila da tuni tana zaune da mijinta , muradin zuciyarta Shamsu , lafiya .

28

Wannan kenan ! BAYAN WATA UKU Da malamin ya haďa gabatar da darasin sa sai ya fita , ďaliban suka mike suka tunkari kofa . Maza suka fara turereniya a kokarinsu na fita daga dakin Caukar darasin , ‘ yam mata a gefe guda sun zuba musu ido . A can bayan ďakin , Hafizu ne a zaune a kan kujera ya dora kafarsa ďaya bisa tebur , kansa a duke yana kallon fuskar wayarsa . Wani matashi sanye da farin yadi tazarce da hula tashi ka fiya naci a zaune a kusa da Hafizu ya mike tare da dora hannunsa a kan kafaďar Hafizu . ” Dan Sanata kowa yana fita don kokarin zuwa gabatar da sallah amma kai gaka a zaune ? ” Hafizu ya dago da kansa ya kalle shi , fuskarsa a yamutse . ” Kuma an fada maka ni kamar kowa ne ? Ni haila nake . ” Matashin ya bushe da dariya kawai sa’an nan yabi ayarin Caliban dake kokarin fita shi ma ya fice . A yanzu kowa ya fice a cikin ajin , Hafizu ne shi kadai ya rage a zaune bai damu yaje ya gabatar da sallah ba . Ta yaya zai fita sallah bayan budurwarsa ta dauke masa hankali da dadadan kalamai masu sanya zuciya nutsuwa a dandalin 2go ? Hafizu yana murmushi , yana sosa kai yana dariya , kwatsam sai jin mutum yayi a tsaye a kansa . Ya daga kansa , a lokaci guda ya tsuke fuska tamkar wanda yayi tozali da mutuwarsa . A tsaye ya ganta a kansa , Hadiza

29

ce ! Tun bayan da ya santa a matsayin ya mace shikenan ya daina kula ta , ko a hanya yaga ta taho to zai saki hanyar da yake kai yabi wata , to tunda yaci moriyar ganga mai kuma zai yi da kwaurenta ? Sai bayan faruwar wannan al’amarin ne ma tsakaninsa da ita ya fahimci ashe bata da body sosai , sa’an nan kazama ce saboda bakinta tsami yake kamar masai , to mai zai yi da kazamar mace ? na ? ” ” Hafizu wai me na maka ne kwana biyu kake gudu Ta ce dashi . Ya daga kai kalleta ransa a bace . ” Nima ban sani ba . Da zaki taimaka mini ki tafi da naji dadi , saboda akwai abun da nake yanzu wanda yafi kasancewarki a nan muhimmanci , bana son takura . ” Hadiza ta kakalo murmushin da a fuskarta ne kawai ya bayyana , amma a zuciyarta kuka take . ” Kada ka damu Hafizu , daga yau in Allah ya yarda ba zan sake zuwa na takura maka ba , nazo gareka ne muyi bankwana . ” ” Mutuwa zaki yi Hadiza ? ” . Ta sake yin murmushi . ” Ko ban mutu ba daga yau ba zamu sake ganin juna ba . ” Ya tattara hankalinsa gaba ďaya gareta . ” Makarantar zaki bari Hadiza ? ” .

30

” Eh haka ne , ammu bani kadui zan barta ba har da kai . ” Hafizu ya zabura . In da abun da yake so a rayuwarsa to baya da karatunsa ne , shine rayuwarsa , shine burinsa , yaji wani abu dake barazanar yi masa katanga ga cikar burinsa . Ya share zufar da ta wanke masa fuska . Cikin dacin rai yace da Hadiza . ya tsani ” Yauslie Babanki ya samu mukamin shugaban makarantar nan ? Na san kusancinki da haka ne zai sa kizo mini da wannan barazanar . ” ” Ba barazana nazo maka da ita ba , nazo maka ne da zahiri . Na san baka manta da extra lesson din da muka yi a watanni uku da suka gabata ba ko ? ” Ya daga kansa kamar mai tumanin wani abu . ” Ta yaya za’a yi na manta da cx tra lesson din da muka yi a ajin dake bayan laboratory , extra lesson me dadi . ” Hadiza ta gyada kai tare da gamsuwa . Ta ja gwauron numfashi sa’an nan ta dan lumshe ido . ” To lokaci yayi da zamu girbi abun da muka shuka a wancan lokacin . ” ” Wake da shinkafa ? ” Ya zuba mata ido . Tayi murmushi . ” Naga sai kwane – kwane kake bayan kuma ka gane abun da nako nufi , abun da nake so na fada maka shine ciki nc dani wata uku ” . A hankali kwakwalwarsa ta fara saka masa zararrukan tsiyar da suka isula a wani yammaci shi da Hadiza, yayi tsammanin yaci bulus! A zatonsa Ya Sha laba! Ashe dai ashe wata rana asirinsa zai Tonu. A’a yaga dai a duhu suka yi abun nan.

Karanta kashi Na 2 Anan 👉

— kuci gaba da bibiyar mu bayan kwana daya domin samun ci gaban wannan littafin — Zaku iyayi mana magana ta wannan lambar ta whatsapp kamar haka +2348105932536

Leave a Reply