Wa’azin Addini

ABUBUWA GUDA HUDU DAKE JANYO BUDEWAR KOFOFIN ARZIKI

ABUBUWA GUDA HUDU SUNA JANYO BUDEWAR KOFOFIN ARZIKI :

  1. TSAIWAR DARE (Qiyamul Layl) : Manzon Allah (saww) ya nuna mana Muhimmancin Tsaiwar dare ya ce tana janyo ma mutum samun girman matsayi awajen Allah. Kuma duk wanda ya hana idonsa barci cikin dare don neman yardar Allah, Shi kuma Allah zai faranta zuciyarsa da rana.
  2. ISTIGHFARI : Allah ya bamu labarin abinda Annabi Nuhu (as) yake gaya ma Mutanensa. Yace :

“NACE (MUSU) KU NEMI GAFARAR UBANGIJINKU DOMIN SHI MAI GAFARA NE. ZAI SAUKAR MUKU DA RUWA DAGA SAMA, KUMA QAREKU DA DUKIYA DA ‘YA’YA, KUMA ZAI SANYA MUKU GONAKI KUMA ZAI SANYA MUKU QORAMU (Wato albarkacin Istighfarin nan Allah zai gafarta zunubanku, kuma zai yalwata arzikinku ta fuskar ‘ya’ya da dukiya da gonakai da Qoramu da kuma ruwan sama mai albarka.

Manzon Allah (saww) yace duk wanda ya yawaita Istighfari Allah zai yaye masa damuwarsa kuma zai azurtashi ta inda ba ya tsammani.

  1. SADAQAH : Sadaqah itama babbar hanyar budewar kofofin Arziki ne. Domin kuwa Allah yana cewa :

“IDAN KUKA BAMA ALLAH RANCHE, RANCHE MAI KYAWU, TO ZAI NINNINKASHI GAREKU KUMA ZAO GAFARTA MUKU.. “.

Kuma yace “DUK ABINDA KUKA CIYAR NA WANI ABU, TO (ALLAH) SHI ZAI NINKASHI KUMA SHINE MAFI ALKHAIRIN MASU AZURTAWA”.

  1. ZIKIRIN ALLAH : Zikirin Allah, Karatun Alqur’ani da Salatin Manzon Rahama (saww) su ke Sanya zuciya ta samu nutsuwa azahiri da badini. Kuma ta hanyar zikirin Allah mutum yana samun yayewar Talauci da Qunci. Kuma yana samun kusanci da Allah da jibintar lamarinsa aduniya da lahira.

Allah yasa mu dace da samun wadannan falaloli. Allah ya yaye mana Quncin rayuwa, ya Qara rufa asiranmu aduniya da lahira Ameeen.

2 Comments

  1. Aliyu salmanu jifatu

    masha’Allah, Allah ya bamu dacewa

Leave a Reply