Labaran Duniya

Southern governors in Nigeria hold meeting with Fulani over pastoralists eviction

Yoruba governors and Fulani leaders are due to hold talks on Monday on the issue of herdsmen’s withdrawal from the southern states of Nigeria.

This dialogue is seen as the first of its kind to bring peace between the two sides.

However, the chairman of the Nigerian Fulani Association, Alhaji Bello Bodejo, said they had not been invited to the meeting because he said the meeting would be useless if the Amotekun giants were not destroyed.

This is the first time that the issue of pastoralists in Ondo State has been investigated since last week’s attack on herdsmen in Rotimi Akeradolu and the alleged attack on herdsmen by Yoruba militants in Oyo State.

Governor Rotimi has accused herdsmen of abducting people in his state.

“Today we have taken major steps to address the issue of kidnappings, as well as other crimes that have been reported in detail by security and media reports and victims in Ondo State. “The governor said.

According to Governor Rotimi: “Many of these problems are attributed to some herdsmen hiding under the guise of herdsmen. “These criminals have turned our forests into hiding places for the abducted people, negotiating with their families for ransom and then releasing them.”

A Yoruba faction, Sunday Igboho, blamed herdsmen for the security situation in the area and ordered them to leave.

The herdsmen, however, denied the allegations, saying they were being driven out by the Yoruba.

President Muhammadu Buhari has also warned the governor of Ondo State against evicting herdsmen from the state’s forests, calling on both sides to come to the peace table.

“There is no alternative but to call on the parties to reconcile and urge the state government and Fulani leaders to continue dialogue for mutual understanding to end the insecurity in Ondo State as soon as possible,” he said.

Presidential spokesperson Garba Shehu later told reporters that they would be on equal footing with any governor who expelled herdsmen from his state because the Nigerian constitution allows all citizens to live anywhere. they want.

You are listening to this article from arewatrending.com and follow us on our social media for the latest world news in Hausa language

(( Hausa ))

A ranar litinin ne ake tattaunawa tsakanin gwamnonin yarbawa da shuwagabannin Fulani kan WA’adin da aka bawa makiyaya Kan ficewa daga jihohin kudancin najeriya.

Wannan tattaunawa ana ganin Irinta ce ta farko da zata kawo zaman lafiya a tsakanin bangarorin biyu.

Saidai shugaban kungiyar fulanin nageriya Alhaji Bello Bodejo, yace ba a gayyace su taron ba domin yana mai cewa taron bashi da wani amfani idan ba a rusa yan kato da gora na kungiyar Amotekun dake korar makiyaya ba.

Wannan shine karon farko na lalubo bakin zaren rigimar dake faruwa tun lokacin da aka bawa makiyaya wa adin barin dazu kan jihar ondo Rotimi Akeradolu ya bayar a makon jiya da kuma harin da ake zargin wasu yan bangar yarbawa sun kai wa makiyayan a jihar oyo hari.

Gwamna Rotimi yayi zargin cewa makiyaya su suke sace sacen mutane a jihar tasa.

“ A yau mun dauki manyan matakai na warware matsalolin satar mutane a hannu daya, da kuma sauran miyagun laifuka wadanda rohotanni kan tsaro da ‘yan jarida da kuma wadanda lamarin ya rusha da su a jihar ondo suka yi cikakken bayani a kansu. ‘’ in ji gwamnan.

Hotan Gwamna rotimi

A cewar gwamna Rotimi: “Yawancin wadannan matsaloli ana danganta su da wasu Bala-gurbi da ke fakewa da sunan makiyaya . Wadannan masu aikata laifuka sun mayar da dazukanmu a matsayin wuraren da suke boye mutanen da aka sace, inda suke tattaunawa da Ahalinsu domin karbar kudin fansa sannan su sake su.”

Hakazalika wani dan bangar Yarbawa Sunday Igboho ya dora alhakin matsalolin tsaron da ke faruwa a yankin kan makiyaya inda ya umarci su su bar yankin.

Sai dai makiyayan sun musanta wannan zargi suna masu cewa kora-da-hali yarbawa suke yi musu.

Shi ma shugaba Muhammadu Buhari ya gargadi gwamnan jihar ta Ondo kan matakin korar makiyaya daga dazukan jihar yana mai yin kira ga bangarorin biyu su hau teburin zaman lafiya.

“Babu wani abin cewa illa kira ga ɓangarorin su yi sulhu da kuma neman gwamnatin jihar da kuma shugabannin Fulani su ci gaba da tattaunawa domin fahimtar juna domin kawo ƙarshen rashin tsaron da ake fama da shi a jihar ondo cikin sauri,” in ji shugaban.

Daga bisani mai magana da yawun shugaban kasa malam Garba Shehu ya shaida wa manema labarai cewa za su sanya kafar wando daya da duk gwamnan da ya kori makiyaya daga jiharsa domin kuwa kundin tsarin mulkin Najeriya ya bai wa dukkan ‘yan kasar damar zama a duk inda suke so.

Kuna sauraron wannan labarin ne daga shafin arewatrending.com kuci gaba da bibiyar mu a Shafukan mu na sada zumunta domin samun ingantattun labaran duniya cikin harshen hausa

Leave a Reply