Labaran Duniya

Ana Kara ci gaba da samun cin zarafin mata a kano

Jami’an hisbah a kano sun koka matuka bisa ga Yadda ake samun karuwar cin zarafin mata da mazaje sukeyi a gidajen Aure a kano.

Hukumar hisbah tace mafi yawan korafe korafen da take yawan samu na cin zarafin mata a kano a gidajen miji ne ko kuma na MAzaje a hannun matan su.

Shugaban hukumar sheik Muhammad Haroun ibn sina, yace lamarin na kara Ta’azzara a yan kwanakinnan,

Ya kara da cewa “Al’amarin na da ban tsoro da ban takaici. Korafe korafen da muke samu sunyi yawa. Sai kaga miji ya Doki matarsa da hannun sa har wurin tashi ya kumbura, ‘’

Namijin da kansa zaije wajan ya nemo Auren matarsa amma wai har ya iya daukar hannu ya mare ta. Duk muna ganin irin haka ana kawo mana kara a wannan hukumar, Cewar kwamandan hisban ibn sina.

Matsalar cin zarafin mata ko ko maza ko yara kanana matsala ce da ke kara ta’azzara a mafi yawan cin kasashe.

Mata da dama kan koka bisa ga yadda mazajen su ke cin zarafin su, inda a wasu Lokutan har ta kan kai ga mummunan rauni a wasu lokutan ma a rasa rai daga bangarorin biyu.

Sheik ibn sina yace duka ba itace hanyar horo da tafi dacewa ba tunda ko a Addini ka akwai hanyoyin da aka ware na yi wa mace horo idan tayi ba dai dai ba.

Akasin yadda akafi gani, a wasu lokutan mata ce ke cin zarafin mijinta ko ma tayi yunkurin kashe shi kamar yadda a kwanakin baya aka samu wasu matan da ake zargin sun kashe mazajen su ta hanyar caka musu wuka.

A zamanin tsohon sarkin kano Muhammadu sunusi na II, sai Da masarautar kano ta gabatar da wani kudurin doka gaban majalisa, kan yadda za’a magance cin zarafin mata, da sauke hakkin iyalai daga bangaren mazajen su.

Saidai haryanzu ba akai ga amincewa da kudurin dokar ba.

A watan yunin bara ne majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa an samu karuwar cin zarafin mata a fadin duniya a daidai lokacin da ake tsaka da kullen cutar korona.

Ana tunanin an samu karin kashi 20 cikin dari a wannan lokaci saboda mutane da yawa na takure a gida da mazajensu ko matansu da ke cin zarafinsu.

Leave a Reply