Labaran Duniya

Yan bindiga sun kaiwa tawagar Gwamnan kano Ganduje Hari A hanyar Zamfara

Ƴan bindiga sun kai hari kan ayarin motocin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje a kan hanyarsu ta komawa gida daga jihar Zamfara.

Kwamishinan yada labarai na jihar Kanon Muhammad Garba ya tabbatar wa da BBC Hausa labarin, kuma ya ce al’amarin ya faru ne a yau Laraba.

Sai dai Malam Muhammad ya ce abin bai shafi Gwamna Ganduje ba domin ba ya cikin tawagar a lokacin da lamarin ya faru, “amma ƴan bindigar sun harbi motoci biyu daga cikin ayarin.

“Sun harbi motar Hukumar Kula da Kare Afkuwar Hadurra ta Najeriya FRSC da ke yi wa ayarin jagora da kuma motar daukar marasa lafiya da ita ma ke yi wa ayarin rakiya,” a cewar kwamishinan.

Ya ƙara da cewa duk da cewa babu wanda ya rasa ransa amma ƴan sanda uku sun ji rauni, kuma dukkansu an sallame su daga asibiti bayan duba lafiyarsu.

Gwamna Ganduje na cikin tawagar gwamnan jihar Jigawa wanda tuni ayarinsu ya yi nisa a lokacin da lamarin ya faru in ji hukumomin jihar Kanon.

“Ƴan sandan tawagar Gwamna Ganduje sun yi musayar wuta sosai da maharan inda aka fatattake su suka koma,” in ji Malam Muhammad.

Wata majiya daga gidan gwamnatin jihar Kano ta ce lamarin ya faru ne bayan da tawagar ta bar birnin Gusau daidai iyakar jihar Zamfara da ta Katsina.

Tuni dai ayarin ya isa Kano bayan faruwar lamarin.

Ayarin gwamnonin Kano da Jigawan suna komawa jihohinsu ne bayan da suka halarci taron sauya sheƙar da gwamnan Zamfara Muhammad Bello Matawalle ya yi daga jam’iyyar PDP zuwa APC a ranar Talata.

Fashin daji

Da yawa daga cikin manyan hanyoyi a arewa maso yammacin Najeriya sun zama tarkon mutuwa, saboda yadda ƴan fashi da ke arkuwa da mutane suka mamaye su.

Hanyoyi irin na Abuja zuwa Kaduna da Kaduna zuwa Funtua, da Funtua zuwa Gusau da hanyar Gusau zuwa Katsina ta wuraren Sheme da Ƙanƙara duk a yanzu sun zama ababen tsoro ga matafiya masu bin su.

Ƴan fashi ba manyan hanyoyi kawai suka matsawa ba, hatta da da garuruwa ba su bari ba, inda suke shiga suna kashe mutane da sace su da ƙona dukiyoyinsu.

Hukumomi dai sun sha nanata cewa suna iyakar ƙoƙarinsu don daƙile maharan, amma har yanzu ana ganin suna ci gaba da cin karensu babu babbaka.

—- kuci gaba da bibiyar shafin ArewaTrending.com domin samun ingantattun labaran duniya cikin sauki —-

3 Comments

  1. Mahamadou Alhassane

    Mahamadou

Leave a Reply