littafan Yaki

Tartsatshin Wuta – Littafi Na 2 (( Littafin Yaki ))

Karan Ta littafi Na farko Anan 👉 (( Tartsatshin wuta – Littafi na 1 Hausa Novels ))

1

lokacin da Shalalatu ta fashe da kuka, sai yarima Irwata ya kama hànnunta yana rarrashinta. “Haba masoyiyata me ya sa za ki ke fadan irin wannan furucin wanda kin san a duk duniya gaba Li daya babu wanda nake kallo na yi tozali da ita na ji dadi sama da ke. Kin sani ke kaďai ce a bar so da kakuna a gare ni rashinki kuma a tare da ni babban hadari ne ga rayuwata gaba ki daya, domin matukar babu ke a doran kasa ba yanda za a yi rayuwa ta dore.” Yarima ya ci gaba da cewa. “Saboda haka don Allah ki bar kawo zancen mutuwa a garc ki domin amincewar Ubangijinmu Allah, kuma alfarmar shugabanmu Annabinmu Allah zai ba mu nasara mu samu abin da za mu tafi nema, domin cikin ikon Allah duk mai nema yana tare da samu. Saboda haka yanu abin da na fi bida a wajenki shi ne addu’arki garc inu, Sannan kuma na tafi da farin ciki da walwalarki domin szmud karfin guiwata a tafiyar tawa zuwa dajin Rukukin. Amma matukar mun tafi ba a son ranki ba to zai yi wuya mu samu nasara a kan abin da muka je nema, sannan watakila kuma rayuwarmu ta salwanta a hanya duk mu halaka yanda ko gawarwakinmu ba za ku gani ba.” Shalalatu tana jin haka ta kara fashewa da kuka. “Don Allah maasoyina ka bar fafan haka domin sai ka dada saka ni cikin damuwa bayan damuwar da nake da ita yanzu. Saboda haka in ka kuma na yı maka alkkawari wallahi daga yau har abada ba zan kara saka damuwa a zuciyata ba in dai a kan maganar tafiyarka ne zuwa dajin Rukuki, balle har wani abu ya samar min kai.” $6 Tana gama fadin haka sai ta kyalkyale da dariya. Da Irwata ya ga haka daga masoyiyarsa sai shi ma ya tintsire da dariya, saboda ta amince da tafiyarsa. “Yauwa gimbiyata ko ke fa ai hakan ya fi. Kuma a yanzu har na ji wani sabon karfi ya shige ni musamman da na ji kin amince da wannan tafiyar da zan yi. Cewar Irwata. Shalalatu ta ce, “Ai dole na amince ya kai sahibina_ saboda ita kan ta tafiyar ma don ni ka shirya ta. Ka ga kuwa idan ban amince ba ai na zama butulu ke nan. Sannan ta kara da cewa. “Ubangiji ya kai ku lafiya ya kuma ba ku abir da kuka tafi nemowa, sannan ya dawo mana da ku gida lafiya. Koda ta zo nan a zancensa sai suka ji sarki yana kiran Irwata. Nan da nan ya amsa kiran mahaifinsa sannan Shalalatu ta ce, “To mu je mana.

2

Haka kuwa ya nke hannunta suka dawo fada. ya je gaban karagar mahaifinsa ya rungume shi. ita ma mahaifiyarsa da suka kira shi gefe suka yi bankwana tare mahaifinsa ya yi masakyakykyawar addu’a, suka rabu da juna suna hawaye Bayan ya dawo cikin fada’yan uwansa gaba ki daya su uku suka ce. “Yanzu đan uwa ba za ka bar mu mu yi wannan tafiyar tare da kai ba Irwata yana murmushi, ya kama hannun kowanne daga cikinsu ya ce. “Ku kwantar da hankalinku yan uwana da yardar Allah za mu je mu dawo lafiya, kuma da abin da muka tafi nemowa, wato ruwan albarka. Malam Ishak ya matso kusa da Irwata ya ce, masa. “Ina fatan dai ba ka manta wannan Kauyen da na maka bayaninsa ba. “Haba malam ya ya za a yi namanta da kauyen Rijau kasar sarkı Larasu Ai ka ce in muka tashi daga wannan garin na mu ka ce gabas za mu yi kuma sai mun yi tafiyar wata uku, bacin zango da dogon hutu kafin mu je Rauyen Rijau wanda in mun je wannan kauyen za mu yiwa sarkin wannan kauyen Larasu bayanin cewa daga Daular Islam muke kuma muna so ya yi mana kwatancen yanda dajin Rukuki yake. Kuma ka ce zai kwatanta mana. Ka ga kuwa ai ban mania ba. Malam Ishak ya yi murmushi, ya ce, “Lallai kuwa haka zancneka yake ba ka mance ba, Allah ya kare ku daga dukkan masifu da balakan da suke cikin wannan dajin. Kuma ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya Nan take malam ya bayar da umarnin aka yi musu addu’a. A take a wajen sannan aka shafa fatiha. Daga na shi ma waziri Garhu ya tofa albarkacin bakinsa da cewa. “Muna fatan Allah Ubangiji ya ba ku nasarar abin da ku ka tafi nema, kuma ya dawo mana da ku lafiya. Ya sa yanda ku ka tafi gaba ki dayan nan lafiya ya maido mana da ku lafiya.” Haka suka hada baki suka ce, “Amin summa amin. Shi kuma sarki Nu’uman bin Imran ya dora da cewa. “Koda yake duk abin da zan ce muku ma a kan wannan tafiyar da za ku yi to liman da waziri sun riga ni sun fada muku. To amma ni ma ba zan rasa abin fada ba.” Sarki ya ci gada da cewa. “Ya kai dana ka kasance mai tsoran Ubangiji a dukkan al’amura na yauda kullum, musamman a cikin wannan hali na tafiya da za ku yi duk irin rintsin da ku ku fada ku roki Ubangijinku kuma da yardarsa zai fitar da ku. Sannan ku yawaita salati ga masoyinmu Annaoi Muhammadu (sallallahu alaihi wasallam).”

3

bayan da sarki ya kare bayaninsa sai Irwata ya ce, “Ya kai Abbana da ha waziri da baba Liman duk na ji abin da ku ka ce kuma zan yi amfani n su insha Allahu, za mu yi aiki da maganarku. Allah ya biya mana bukatunmu na duniya da lahira alfarman manzonmu. Da duk aka gama wannan tattaunawar sai Irwata ya yi sallama da kowa da kowa, domin ya ce ba sa bukatar kowa ya yi musu rakiya zuwa bayan cari, gudun ka da sahibasra Shalalatu da kuma yan uwansa uku ya su ce za su bi shi. Haka ya hau kan dokinsa yana zubar da hawaye, suma ‘yan uwansa da masoyiyarsa Shalalatu suna yi sabada shakuwa. Sannaan ya shiga gaban wannan runduna ta sadaukai dubu goma, ya yi musu jagora suka fita daga cikin wannan kasar ta Daular Islam. Da suka fita bayan gari sai suka saki linzamin dawakansu suka nutsa gabashin kasar ta su ta Daular Islam. … … A can kasar Shallu kuwa wato garin sarki Illatu kwance tashi har matarsa daya ta samu ciki, wato gimbiya Gariyatu. Ai kuwa da samun cikin na Gariyatu, murna a wajen sarki Illatu ba ta musaltuwa. Domin tun fitowar cikin fili sarki ya inana Gariyatu yin kowanne irin aiki a cikin gidan na saruta, saboda ba ya so ta rika shan wahala ko `yar kadan. Kuma sauran matan sarki guda biyu da suka ga haka wato irin wannan tattalin da sarki yake yiwa kishiyarsu wai don kawai ta samu juna biyu, alhali su kuma ba ya nuna musu haka. Kawai sai suka hadewa Gariyatu kai su biyun suka ji sun tsane ta komai ta yi sai tsangwama da zagi tare da cin mutuncinta. Ita kuma da yake Gariyatu maçe ce mai hakuri sai tabar abin a rantga babu wanda ta fadawa, muzgunawar da kishiyoyinta suke yi mata hatta shi kansa sarki Illatu ba ta fadawa ba domin ta san in har ta sanar da sarki irin halin da take ciki to ta san ba zai yi musu dadi ba. Kai in ma har bai kore su daga gidan ba saboda ta san zai iya yin komai a kan wannan ciki da ta samu, musamman da suke takura mata a kan abin di sarkin ya fi kauna a duniya, wato cikin da take dauke da shi. Gariyatu ta riga ta san yanda sarki yake ji da wannan ciki na jikinta to lallai ba makawa zai iya halakar da mutum a kansa musamman da ta yi la’akari da yanda ya dade yana nema bai samu ba sai a wannan lokacin da ya aure su. Shi ya sama kawai take yin bakuri da duk abin da suka yi mata ta riga dai ta san ba su isa su hanata haihuwa ba. Wata rana Gariyatu tana

4

dankishingide a dakinta a kusa da ita ga wani faranti a cike da va’van inubi da ruman da kuma tufa, a gefenta kuma ga kuyangarta mai suna Shaluhatu Kuyanga Shaluhatu ta dubi uwargidanta ta ce, Yanzu uwar dakina haka za ki zuba ido ke nan ana ci gaba da muzyuna mi ki a cikin gidan nan alhali kina da juna biyu? To ya kama ta fa maimartaba ya san halin da ki ke ciki. domin abin ya yi yawa, gaskiya ba a kyale ki ba haka mu kuyanginki ba kyale mu ba. Da Garıyatu ta ji haka daga bakin kuyangarta Shaluhatu sai ta yi hakuri, domin ta gado mahaifinta sarki Gazzu wajen hakuri. Koda yake ita ba musulma ba ce domin tun daga kan sarki lMatu da kuma sarki Gazzu tare da wadannan sarakuna guda arba’in da bakwai babu musulmi a cikinsu duk gaba ki daya arna ne domin ba sa bautawa komai. Ma’ana dai ba su da addini. To duk da cewar Gariyatu arniya ce wato ba ta bautar komai, sai kuma Allah ya yi ta mace mai saukin kai wanda ko kadan ba ta dauki duniya da fadi ba. Sannan Allah ya zuba nata bakuri a zuciyarta zai yi wuya ka ga an mata ta yi tsiwa, tunma tana budurwa, sai ta dauki abin ba komai ba balle ta ce za la hukunta wanda ya yi mata hakan a cikin kuyanginta. Shi ya sa a lokacin da take gida duk kuyangar da sarki ya ba ta ba karamar murna kuyangar take yi ba na zamantowarta hadimar Gariyatu Sannan ga son kyauta a cikin Gariyatu tun yanda take daukan kanta kuma duk kyawun kaya kuma komai tsadarsa za ta iya dauka daga gare ta ta bawa wata daga cikin kuyanginta kyauta kuma ba ta tsangwamar kuyanginta ko kaďan. Sannan Gariyatu tana iya daukar kudi ko nawa ne ta bawa kuyanginta kyautarsu. Saboda haka kuyanginta tare da mutanen gari suna matukar kaunar Gaariyatu sun fi son ta duk cikin ‘ya’yan sarki Gazzu. Bayan haka uwa uba shi ne tarbiya da ta samu daga wajen mahaifinta sannan kuma ko kaďan ba ta tsallake umarinin inahaifinta ba su taba sata wani abu ta ki yi ba. Bayan wannan Gariyatu ta dade tana sha’awar shiga addinin musulunci, musamman kuwa da ta fahimci cewar shi ne addinin Allah na gaskiya da ya aiko manzonmu da shi. Koda yake ya kasance dama a cikin samari masu zuwa wajenta kafin ta yi aure hadda wani musulmi dan kasar Daular Islam mai suna Anru

5

Anru ya kasance saurayi ne kyakkkyawa, kuma aboki ga dan sarkin ar wato yarima Irwata. Tun a shekarun baya da suka gabata Anru ya bar Casar Daular Islam ya tafi wata kasa mai suna Shatta zuwa wajen neman limin karatun Alkur’ani mai girma. Da kuma sauran manyan litattafai. Anru sun hadu da Gariyatu ne a bayan garinsu da ita Gariyatun. Wata rana Gariyatu tana tafiya a bayan garinsu ita da kuyangintsa a Jokain sun dawo daga yawon kilisa ne ita da kuyanginta. Kawai sa ta ga wani kyakykyawan saurayi a cikin wani dan kogo yana wani abu mai kamar dai abin musulmai sukc yi wato sallah, ta wajen kogon kuma ga dokion wannan mutumin yana kiyo. Tunda gimbiya Gariyatu take ba ta taba ganin mutummin da son sa ya yi dirar mikiya tashi daya a zuciyarta ba kamar wannan bawan Allan da ke sallah a wannan kogon dutsen. Nan take Gariyatu ta tsaya a kusa da wannan kogon tana kallon wannan bawan Allah da ke ibadarsa domin a wannan lokacin tana jin tsananin kaunarsa ne tana shiga zuciyarta. Su da kansu kuyanginta suka tsaya su kuma suna mamakin ta wato ita Gariyatun saboda tunda suke da ita ‘ya’yan sarakai da ‘ya’yan attajirai da dama sun nuna mata so, samina ba ta amince da ko mutum daya ba, amma ga shi wannan bawan Allah da ta gani ba ma magana ya yi mata ba ita kuma ta tsaya tana kallonsa wanda ga alama wannan kallon na so ne da kuma kauna. Haka dai kuyangin gimbiyar suka dinga kissa wannan a cikin zukatansu har wannan bawan Allah ya gama wannan ibadar tasa. Koda ganawa sai ya dago da kansa ya ga Gariyatu tana kallonsa sai kawai ya ji gabansa ya fadi, saboda ganin kyawunta wannan budurwar. Ita kuma Gariyatu tunda wannan bawan Allah ya dago suka hada ido sai ta sunkuya ba ta kara dagowa ba domin kunya. Shi kuma wannan saurayin da ya ga haka sai ya yi murmushi, sannan ya fito daga cikin wannan kogo na sutse. Ai kuwa yana fitowa waje da Gariyatu ta kara kallonsa sai kawai ta dada rudewa domin ta ga kamar shi ya yi kansa saboda saurayin fari ne sannan ga shi da ‘yan kananan idanuwa masu kyau da dan madaidaicin hanci, sannan yana da baki mai kamar yankan reza, ga shin kansa kwantacce ne irin na Larabawa, saboda shi ma wannan saurayin Balarabe ne. lowa waje da Gariyatu ta kara kallonsa sai kawai ta darfa rudewa domin a ga kamar shi ya yi kansa saboda saurayin fari ne sannan ga shi da ‘yan

6

kananan idanuwa masu kyau da dan madaidaicin hanci, sannan yana da baki mai kamar yankan reza, ga shin kansa kwantacce ne irin na Larabawa saboda shi ma wannan saufayin Balarabe ne. Bayan da wannan saurayin ya fito daga cinin wannan kogon na dutsen sai ya je gaban gimbiya Gariyatu ya ce, “Amincin Allah ya tabbata a gare * ki sarauniyar kyawawan duniya, lallai Allah ya yi halitta a nan .tsarki tabbata ga Ubangijin da ya tsara wannan kyakykyawar halittar wanda don haske har kyalkyali take yi.” Haka dai wannan saurayi ya ci gaba da koda kyawun Gariyatu ita kuwa sai murmushi take yi da jin baka saboda yaboin ta da ta ji ya yi da babu wani mahaluki da ya taba yi mata haka sai shi a karo na farko. Da wannan saurayin ya yi shiru sai Gariyatu ta ce masa. “Ai kai ne shugaban kyawawa na duniya, saboda kai ne wanda haskenka ke’dusashe hasken rana da wata, don tsananin kyawunka. Kuma kai ne saurayin da in har za a fita takarar neman shugaban kyawawa na duniya, lallai ba shakka dole ka cinye gasar.” Sannan ta dubi kuyanginta ta ce musu. “Ku dđan koma gefe domin ina so mu yi wani siri da shugaban kyawawa na duniya.” Nan take kuyanginta suka bi umarnin ta suka tafi suka konia can gefensu domin ba su damar su tattauna a tsakaninsy wato a tsakanin gimbiya Gariyatu da kuma wannan wanda take yabonsa duk da cewar dai abin ya ba su mamaki sosai domin tunda suke da gimbiya ba su taba ganin ta rude da ganin kyan wani da namiji ba sai yau, saboda ita ma ta kasance allura cikin ruwa mai rabo ka ďauka. Saboda kyau domin duk a nahiyar kewayen garuruwan nan babu wanda ya kama kafarta ma ko a rabin kyau na Gariyatu domin ita ce tauraruwa a cikin tauraria mata. ya Bayan tafiyar kuyangin daga wajen saurayin sai Gariyatu ta dubi wannan saurayin har ta bude baki za ta yi magana sai ta ji kunyarsa ta rufe ta. Da shi kuma wannan saurayin ya ga haka sai ya ce, “Ya ba ki fadi abin da ki ke son fada ba shugabar kyawawa ta duniya.” Da gimbiya Gariyatu ta ji haka daga bakin wannan saurayin sai ta ce, “Aminci tare da yadda su tabbata gare ka ya kai wannan saurayin ma’abocin kyau da annuri, ai dole ganin wannan kyakykyawar fuskartaka ta mantar da mutum daga wani lafazi da ke cikin zuciyarsa ya yin da yake shirin firta shi.

7

Amma tunda dai barin kashi a ciki baya maganin yunwa ya zama dole vanzu na sanar da kai abin da cikin zuciyata duk kuwa da cewar shi wannan abin da zan sanar da kai bai zama lallai ka amince da shi ba. In na vi la’akari da cewa ba addininmu daya da kai ba. Wato ma’ana ni ba musulma ba ce. Gariyatu ta ci gaba da cewa. “Tunda nake a duniya ban taba furtawa da namiji wannan maganar da zan furta maka ba duk kuwa da cewa ‘ya’yan sarakai da kuma attajirai na wa su kashen ba ma wannan kasar ba sun nemi na furta musu. wannan kalamin da zan furta maka amma zuciyata ba aminta da hakan ba.” Gariyatu ta dan tsaya ta yi murmushi, sannan ta dora da cewa. “Amma kai farar daya da idona ya yi tozali da kai nan take na ji zuciyata ta amince da kai. wWato ba komai nake son fada maka ba ya kai wannan saurayi ma’abocin kyau illa na sanar da kai ka riga ka shiga cikin zuciyata tana son ka nema mata matsugunni a cikin taka zuciyar. Ma’ana tunda nake a duniya ban taba jin son da namiji ya shiga zuciyata farar daya ba sai yau da na yi tozali da kyakykyawar surarka. Lallai ya kai wannan saurayın na ji saonka ya ratsa zuyciyata da duk ma ilahirin jikina. Da fatan kuma kamar yadda na nuna maka maitata a fili a kan sonka haka kai ma za ka yi saurin amincewa da batuna. Bayan da Gariyatu ta gama fadar wannan maganar ga wannan saurayin sai shi saurayin ya dada yiwa wannan budurwar murmushi, sannan ya ce, “Ba kowane da namiji ba ne wanda zai gan ki bai yi burin mallakarki a matsayin matarsa ba domin duk abin da ake nema ga ‘ya mace tabbas in an zo wajenki an gama samu. Saboda da duk wata sura ta kyau Allah ya ba ki ita saboda haka sai ki kara godewa mahaliccinki da wannan baiwa ta kyau da ya yi mi ki don ba kowane bawan sa ne yake samun haka ba.” Sannan wannan saurayiin ya ci gaba da cewa. “Kuma zancen da ki ka yi na cewar kiná so na hakika ni ma na ji ina kaunarki amma sai dai wani banzari ba gudu ba ke ba kya cikin addinina wato addinin gaskiya na musulunci, duk kuwa da cewar auren na ki bai haranta a gare ni ba. Shi dai addinin musulunci kai da ka ke cikinsa ka auri, (AHALUL KITABI). Ma’anar ahalul kitabi wato, wadan da ba sa cikin addininka koda kuwa suna da wani addinin na su na daban da suke yi. Domin mu a wajen mu musulmai da wanda yake bautar taurari da mai vautar gumaka da kuma wanda ba su da addinin kamar misalin ku ke nan

8

mutanen yankin garuruwan nan gaba ki daya, duk ku mu a wajen mu sunan ku arna, tunda dai ba kwa bautawa Allah, mahaliccin sammai guda bakwai da kassai bakwai da duk halittin da suke cıkin wannan duniyar gaha ki dayansu. Da Gariyatu ta ji haka daga bakin wannan saurayin sai ta ce, “Na ji Juk abin da ka ce. “To amma ina so ka sani cewa dama tun ba yau ba nake sha’awar wannan addinin na musulunci, kawai dai na rasa wanda zai sanar da ni yanda za a yi na shige va ne. Amma yanzu na yi maka aikawari zan shiga wannan addinin na muslunci, domin na dade ina son zama a cikinsa. Da wannan saurayin ya ji haka sai va dubi wannan budaurwa ya ji wani farın ciki, ya mamaye shi musamman da ya ji wannan budurwar ta sanar da shi cewa ita ma tana son ta inusulunta. A nan kuwa ya sanar da kowa suņansa sannan kuma Gariyatu ta ce masa “Ya ba ka ce komai ba kuma a kan zancen soyayyata da na firta maka cewa ina kaunarka a cikin zuciyta?”Anru ya ce, “Ai na amince da soyayyarkı kuma za mu dinga haduwa a nan bayan gari, duk bayan mako, mu fara tattaunawa a kan maganar auren mu. Gariyatu tana jin haka ta kyalkyale da dariyar farin ciki don jin Anru-ya amince zai aure ta. To a haka dai suka dinga yin soyayya a boye ba tare da sanin mahaifinta ba. To a dai-dai lokacin da Gariyatu take shirin shiga addinin musulinci ta hannun saurayinta Anru sai wani al’amari ya faru a lare da ita. A wannan lokacin ne mahaifinta ya furta ma ta zancen auren shugabansa sarki llatu ita kuma Gariyatu da yake mace ce mai hankali da kuna son abin da zai farantawa mah.aifinta rai sai kawai nan take ta amince da batun mahaifinta duk kuwa da cewa ita ba haka ta so ba. Tun daga wannan ranar da inahaifinta Gariyatu ya bada aurneta ga sarki Illatu ita Gariy atu ba ta vadda ta kara fita bayan gari ba gudun kar ta hadu da saurayinta Anru. Koda vake ita ma ba son auren take ba sai dai ta dade da yiwa kanta alkawari, kanaI yanda mahaifinta yake nuna mata gata da o) ha kuna kauna, to ita nra alkawari ta dauka a zuciyatrta ba ta taba sabawa umarnin mahaifinta ba duk lokacin du va furta mata hakan. Wannan shi ne babban dahhba da va u da mahaifinta ya yi mata maganar auren shugabansa saarkt lilatu ta amince masa lokaci daya A wannan ranar ta sha kuka har ta gaji, da ta ji 7a a raba ta da masoyinta. amina haka dole ta hakura aka yi aurenta da babban sarki wato Illatu.

9

Yau kusan tsawon shekaru biyar rabanta da shi. Haka dai Shaluhatu ta ci gaba da bawa gimbiya gariyatu shawarar ya kama ta ta yi gaggawar sanar da sarki irin wannan takurar da ake yi mata a gidan sarautar domin gaskiya abin ya yi yawa sosai. Gariyatu ta yi murmushi. “Amma Shaluhatu har kin manta duk mutum mai hakuri ko bade ko ba jima zai ga amfanin wannan hakurin da ya yi. Saboda haka kar ma ki sa wani abu a ranki wata rana duk wadannan abubuwan za su zama tarihhi.” Da kunyagta ta ji haka daga bakin shugabarta Garıyatu sai ta ce, “Yau ba zan kara fadan wannan magar ba kuma wannan hakurin da ki ke da shi tamkar dabi’un musulmai ne wato irin addinin musulunci ne. Gariyatu ta kara yin murınushi, sannan daga bisani sai ga hawaye yana gangarowa daga idanuwanta. Da Shaluhatu ta ga haka sai hankalinta ya tashi domin tunda suke da gimbiya ba ta taba ganin tana kuka ba sai a 64 wannan ranar. Bayan kuyanga Shaluhatu ta gama wannan jimamin na kukan gimbiya sai daga bisani kuma ta cewa gimbiya. *“Yake uwar dakina ‘yar sarki jikar sarki me ya same ki da har wannan kyakykyawar fuskar take zubar da hawaye?” Bayan Gariyatu ta ji wannan tambayar daga bakin Shaluhatu sai ta sa hannun ta goge wannan ruwan hawayen da ke zarya a kumatunta sannan ta maida kallonta ga kuyanga ta ce, “Yake Shaluhatu ba komai ba ne ya sa ni zudda hawayc ba sai dan tunowa da masoyina da na yi ma’abocin addinin musulunci wanda kuma ya so na musulunta a hannunsa domin bin tafarkin gaskiya. Domin na dade da sanin shi wannan addinin na islama shi ne̟ addinin Allah na gaskiya, kuma wanda ya aiko manzanninsa a kai musamman jagoransu Annabi Muhammadu. Sannan Gariyatu ta ci gaba. “Duk wannan bayanin da ki ka ji na yi mi ki na same shi ne daga bakin masoyina abin kaunata wato Anru ma’abocin addini mai tsafta na musulunci, wanda dole ta sa na rabu da shi ba don na soba sai don ba na son in tsallake umarnin mahaifina Amma yanzu haka ina ji a jikina cewar za mu dada saduwa da masoyina Anru kuma ina mai tabbatar mi ki yake Shahulatu matukar mun hadu da masoyina Anru bayan na haifawa sarki wannan cikin to ba shakka zan bị shi zuwa kasarsa na bar abin da na haifia a wajen sarki tunda dama shi babban burin sa ke nan samun magaji, wanda zai gaje shi koda bayan babu

10

shi daga doran kasa. A wanda hakan shi ne makasudin aura mana shi ni da ‘yar uwata Haflatu Kuyanga Shaluhatu ta ce, “Ai ni na da ki ke gani na yake yar uwar dakina na dade ina sha’awar shiga wannan aaddini na musulunci, to amma darnar hakan ba ta samu a gare ni ba har yanzu a matsayina na baiwa wacce ba ni da ‘yancin aiwatar da wani abu matukar ba masu iko da ni ba wato Gimbiya tana murmushi, ta kama hannun kuyanga Shaluhatu. “Yake yardaddiyar kuyangata ina mai tabbatar mi ki da yaddar Ubangijin musulunci ba makawa sai na cika mi ki wannan burin na ki na shiga cikin addinin musulunci. Saboda haka ki kwantar da hankalinci Da Shaluhatu ta ji haka daga bakin uwargidanta sai ta kasance cikin farin ciki da kuma annuri domin dama ta dade tana sha’awar shiga addinın musulunci, hanyar shigar ne habu a matsayin da ta taso na baiwa tun tana karama wato tana bauta To haka dai Shaluhatu suka ci gaba da tattaunawa da uwar gidanta a kan yanda za su shiga addinin musulunci Kwance tashi babu wuya a wajhen Allah, har lokacin haihuwar Gariyatu ya yi kuma da vardar Allah da anincewarsa ta haihu latiya kuma ta haifi kyakykyawan yaro, fari mai suffa irin ta ta wato ita mahaifiyar tasa Sarki llatu saboda muma lare da fari cikin har ku san hauka ya yi saboda abin da ya jima yana nema sai ga shi yanzu ya samu. Kai sarki Illatu haka ya rika fitowa da dukiya daga bitalmaninsa yana rabuwa jama’a. Abinci kuwa sai da ya daukewa jama’ar kasarsa na tsawon kwana uku. wato a duk wadannan kwanaki ukun ba talaka da ke wannan K isa duk mutanen kasar sarki ne ya ba su abincin tsawon wadannan kwanaki ukun Haka sutura ma sarki ne ya rinka rabonta a wannan rana ta haihuwar matarsa Gáriyatu. Kuma ga shi ya samu da namijin da yake so domin gadon wannan sarautar tasa. Ita kuwa kuyanga Shahulatu da ta kaiwa sarki albıshir din haihuwar Gariyatu nan take sarki Illatu ya ‘yanta ta ya ce, “Daga ranar ta zama ba baiwa ba ta zama mai bawa matarsa Garıyatu shawara, a kan al’amuranta na rayuwar yau da kullum Kuma dama tun da dadewa Gariyatu ta taba cewa mijinta sarki Illatu da zarar ta haihu to ra ta ʼyanta kuyangarta. To kuma sai ga shi sarkin ya cika mata burinta na’yanta Shahulatun lun kafin itan ta ‘yanta ta. Sannan kuna sarkin ya bawa Shahulatu kyautar dinare dubu da kuma dawakai guda uku da tufafin sawa kala goma duk a

11

Matsayin tukuicin albisihir din da ta kawo masa na haihuwar matarshi Gariyatu Ita kuma Shahulatu ta yi fain ciki sosai da wannan kyauta da sarki ya yi mata a matsayin tukuici, sannan ta yiwa sarkin godiya sosai da wannan abin alherin da ya yi mata. Su kuwa kishiyoyin Gariyatu su biyu wto uwaragida Harkatu da amarya Hatlatu ina wuta su saka dan da kishiyarsu Gariyatu ta haifa don bakin ciki. Haka su biyun suka zauna a dđakin Harkatu domin tsegunta munafincinsu a kan ‘yar uwarsu wato abokiyar zamansu Gariyatu. Bayan sun zauna din sai amarya Haflatu ta dubi kišhiyarta ta ce, “Yanzu yaya ta haka za mu zubawa Gariyatu ido tana abin da taga dama don kawai ta haifawa maimartaba da, sannan fa kar ki manta yaya ta shi ke nan fa duk wani sirrin sarki zai koma gare ta tunda dai ta haifa masa abin da yake nema tunda dadewa. Ki dubi fa shekarun da kuka yi da mijinki amma ga shi lokaci daya ya juva mi ki baya don kawai wannan shegiyar ta zo ta haifa masa abin da yake so. To lallai ya kama ta mu tashi tsaye mu ga mun magance wannan matsalar tun ma kafin abin ya yı nisa don in muka tsaya muka zuba ido za a yi ma na sakiyar da babu ruwa. Haflatu ta ci gaba da cewa. “Ki ga fa tun yanzu ke nan da ta haihu irin bushashar da sarki ya yiwa jama’ar kasar nan kuma har ya dauke mu su haraji na tsawon wasu watanni wanda su da kansu har fada suke tunda suke ba su taba ganin wannan haihuwa da Gariyatu ta yi to yanzu ma ke nan ina kuma ga dan in ya girma saboda haka yayata tun yanzu gwara mu san abin yi ga wannan al’amari. Harkatu ta janye hannunta daga tagumin da ta yi, sannan ta kai kallonta wajen Haflatu. “Kan wata ai ba ki san yanda nake jin abin nan a zuciyata ba tamkar wani mashi aka caka min a kahon zuci, haka nake jin wannan abin domin tun ranar da Gariyatu ta samu juna biyu tun daga wannan ranar bacci va kauracewa idanuwana in ban da yawan tunani da yawan damuwa babu abin da ke makare da zuciyata musainman kuma da a kai wannan haihuwar sai abin duk ya z0 ya kara dagulewa, ya fi da Domin yanda na ga sarki yana rabon dukiya a ranar abin har tsoro ya ba ni. To yanzu he nan ina kuma ga dan in ya girma don yanzu so da tattakin sarkı zai kona ga wannan yaro. To amma kar ki damu kanwata ki kwantar da hankalinki domin na ďaukar mi ki alkawari ko ta halin yaya zan san

12

yanda zan y i sai na ga bay an wannan da da Garıy atu ta haifawa varki ko kuma na ga bavan ita kanta mahaitiyar ta va Domin akwai wani bakona da yake mnın aikı a duk lokacin da bukatar suka taso kuma da zarar ya yi min nake ganın bıyan bukata nan take. Don haka dazarar sarki gobe ya fita mu ma sai mu fita mu tati zuwa dajin da bokan nawa yake don sanar da shi abin da yake faruwa. Haflatu ta kyalkyale da dariya saboda dadin da ta ji na wannan maganar sanna ta ce, “Yanzu dama yayata kin san da wannan bokan na ki amma tun farko ki ka ki ki sanar da ni kawai hanyar da ya kamata mi bi ke nan wajen ganin mun salwantar da rayuwarta ko kuma ta jaririn da ta haifa Haflatu ta ci gaba. Na natsu sosal gabe ta yi domin zuwa isar da burin nan na mu. A kashe garin ranar kuwa sarki ya hau ya tafi rangadi garin sarkińsa wato sarki Gazzu Bayan tafiyar sarki da tsawon sa’a daya suma matan sarkin guda biyu uwargida da amarya suka yi badda kama suka hau dawaki biyu suka kama hanya har suka je kofar fita a garin masu gadin kofar mutum uku suka tare su suna tambayarsu su su waye? To da yake duk zuciyarsu a bushe take babu tsoro, a cikinta sai Haflatu ta vi gyaran murya ta ce musu “Muna daga cikin tawagar sarkı kuma da mu uka shirya w.nnan tafivar zuwa rangadi To a lokacin da za su tafi sai sarki ya’ samu wani aikı ya ce mana in mun gama mu riske shi a kasar sarkinsa sarki Gazzu sannan mu shiga saurarn garuruwan. Da wadannan dogaran kofar suka ji wannan maganar daga bakin Haflatu sai suka amınce, kuma suka bude musu kotar suka fita daga cikin garin suka nutsa daji su biyu. Can suna cikin tafiya sai Haflatu ta ce, “Gaskiya yayata kina da dimbin basira musamman da ki ka fadi wannan maganar ga masu gadi, ba tare da shakka ko wani kokonto ba. Da kuma canja murya da ki ka yi. Harkatu ta yi murmushi. “Ai kanwata in ki ka ji ana tsoron a bu to mai (soronsa ne ba shi da kekashashshiyar zuciya. Amma a yanda ni din nan zuciyata take a yanzu babu abin da ba zan iya ba wajen ganin bukata ta ta biya. Kuma ban san lokacin da wannan dibarar ta zso min ba na fadan wannan maganar kawai ni dai ji na yi muryata ta zama ta maza ina furta wannan maganar kuma, ga shi sun amince da haka, wannan alama ce ta cewa akwai nasara a tare da mu. Sannan Haflatu ta ci gaba. “Yake kanwata a yanda nake ji na yanzu da zuciyata ta zama babu imani in dai a kan Gariyatu ne ko kuma jinjirinta to

13

zan iya yin komai, ciki kuwa hadda salwantar da rai ko na wane ne in dai a kan hakan ne. Haka dai suka dinga hira suna tatiya har suka je wannan Jajin da wannan bokan yake Tsakanin dajin da wannan boka yake da Parin sarki llatu tafivar kilo mita biyar ne sai-dai kuma wannan bokan yana cikin wani kogo ne da ke da tsananin duhu kuma kogon yana kusa da wata katuwar bıshivar tsamiya. Da zuwa sU harkatu gındin wannan bishivat wato kusa da wannan kogon sai ta gunduma wata shar ita harikatu wanda wannan ashariyar ita Ce Sallama A wajan wannan bokan da suka zo wajen sa. can jimawa sai ga wata kakkartar iskja ta taso gami da rugugi maI tirgitarwa To da yake ita amaryar sarki Haflatu ba ta saba ganin haka ba sai ta dan rAtana kadan, amma Harkatu ta ce ta kwantar da hankalinta hokan ne zai hayyana, kuma dama duk lokacin da zai bayyana gare ta sai ya yi haka Suna cikin yin wannan maganar sai kawai ga boka Harjiru ya bayyana daga shi sai fatar giwa da ya rufe, al’aurarsa da ita. Amma sauran jikinsa duk a waje yake. Sai dai akwai guraye a daure a wuyansa da kuma kunkuminsa. Sannan ga wasu a daure a damatsansa da kuina kansa. Bayan boka Harjiru ya yama bayyana sai ya zauna a gindin wannan bishiyar’ tsamiyar sannan ya umarci bakinsa suma suka zauna. Ai kuwa haka aka yi suka zauna a kusa da shi. Bayan sun zauna sai boka Harjiru ya ce, “Ranki ya dade ki ce ku ke tafe yanzu, ai yanzu `yar karama ta bar nan gun kuma ita ta sanar da ni zuwanku. Dama dalilin da zai kawo ku na cewa kuna so, ko dai a kashe dan da Gariyatu ta haifa ko kuina a dauke ita kanta mahaifiyar ta sa a haukakata ta bar garin. Harkatu ta ce, “Boka duk abin da ka ce haka ne kuma muna so ne ai mana aiki da gaggawa kamar yanda na sanka da domin shi wannan aikin da za ka yi min ya sha banban da sauran ayyukan da ka ke yi min a baya. Saboda haka ka san kuwa dole ladansa ya nunka na su yawa nesa ha kusa ba Boka Harjiru ya tuntsire da dariya, ya ce, “laka yake sarauniya, ainya gidan sarki llatu da kuma kishiyarkı ita ma shugabar kyawawa ta sarki Matu w ato kishiyarki Haflatu gata nan a kusa da ke. Da ya gama fadan haka sai Haflatu ta ce, “Boka ka san wannan aikin da za-ka yı mana ni da yayata aikı ne mai matukar mahimmanci a gare mu.

14

Sahoda haka matukar wannan aiki da za ka yi mana ya yiwu kana da lada mai tsoka ta bangarena Da wannan bokan wato boka Harjiru ya ji haka kuma du daga bakin Haflatu sai ya kuma bushewa Ja wata hamahaukaciyar dariya sai da ya yi ta ishe shi, sanan ya yi shiru Sannan ya ce, “Yanzu kuwa da amincewar dan Matsutsu zan yı muku aikin da za ku yaba da shi. Nan take boka Harjiru ya fara sanbatu da wani tsatsube-tsatsube har tsawon kusan minti talatin, sannan daga bisani ya dago ya dubi su Harkatu ya ce musu. Hakika aljanu wato ruhanai na sun faďa min shi wanann yaron da ku ke son kashewa ba zai taba mutuwa a hannunku ba domin in ya gima zai zama gagarumin sadauki wanda duk lardin nan ba za a samu ya shi ba. Kuma bayan haka ba a fadar kasar ku zai girma ba har ya shiga addinin musulunci ba. Zai rayu ne a can wata kasa ta musulmai, amma daga baya bayan ya girma zai ce zai bi duk kasashen karufai ya juyar da su zuwa addinin da yake kai na musulunci, ciki kuwa hadda kasarsa ta haihuwa, wato kasar ku. Sannan kuma da sauran kasashe guda arba’in da takwas din nan da ke wannan bahiyar ciki kuma hadda kasar ku. Ke Haflatu da kuma kasar su mahaifiyarsa. Sai dai kuma ba zai taba samun nasara a kan hakan ba saboda wani babban dalilin da za ku sanu labarin daga baya.” Sannan bokan ya ci gaba. “Ita kuma mahaifiyarsa Gariyatu nan gaba kadan akwai abin da zai sa ta bar kasar zuwa w ata kasa ta musulmai wanda a can za ta musulunta sai dai hadimai na ba su nasar da ni makasudin barinta garin na ku ba sun ce min ko shekara ba za a yi ba tare da wannan jaririn da ta haifa za su tafi ba. A wannan lokacin ita kadai za ta tafi amma shi kuma jaririn na ta sai bayan wani tsawon lokaci ya bar fadar kasar ta ku kamar yanda na sanar da ku a baya ba zai girma a cikin masarautar ku ba. Saboda haka yanzu me ku ke so a yi muku? Za a bari ne har lokacin da ita da kanta za ta bar kasar ta ku ko kuma dai a yi muku abin da za ta tafi a gobe?” Harkatu ta ce, “To kanwata kin ji abin da boka ya ce amma ke me ye shawararki a kan haka?” Haflatu ta ce, “Ni dai a shawarata tunda har akwai sanadin da zai sa ta bar wannaan kasar to mu kyaleta kawai har lokacin ya yi. Wanda in ta tafi ta tafi ke nan har abadaba ita ba dawowa wannan kasa ta mu. Saboda duk

15

Son da sarki yake mata matukar ta shiga cikin addinin musulunci sun rabu ke nan har abada. Shi kuma danta da za ta bar shi ya girma a hannunmu to bayan ya girma wahalar rayuwa ma sai ta sa ya fita ya bar masarautar ubansa da kansa. Harkatu ta dubi Haflatu suka kyalkyale da dariya su biyun. “Hakika kanwata wannan shawarar ta ki’ta yi saboda hakan za a yi mata komai.” Da boka Harjiru ya ji haka sai ya kyalkyale da dariya mai amon sauti sai da ya yi ta isheshi tukunna sannan ya ce, “To shi ke nan ranki ya dade tunda baka ku ka zaba.” Nan take Harkatu da kishiyarta wato Haflatu suka bawa boka Harjiru kudi mai yawa sanan suka yi godiya suka tashi suka koma zuwa garinsu. Da suka je bakin get din shiga garin na su sai masu gadin suka durkusa Suka gaishe su domin a wannan lokacin ba su 6adda kama ba. Sai masu gadin suka ce, “Ranki ya dade ina ku ka je kuma ba tare da masu rakiya ba? Ko kuwa dai kuna cikin tawagar sarki ne a fita rangadin da ya yi?” Harkatu ta daka musu tsawa ta ce, “Ina ruwanku da wajen da muka je da za ku dame mu da tambaya. Kanwata kyale su zo mu tafi.” Suka wuce suka bar masu gadin a durkushe. *** Wata rana Harkatu ta shiga dakin Gariyatu ta ce, mata. “To munafuka shi ke nan burinki ya cika na haihuwa ga maimartaba. To ina mai tabbatar mi ki ko ʻya’ya dubu ki ka haifa tsotsonki ba zai taba mulkar kasar nan ba.” Sannan ta juya ta tafi. Ga fitarta Shaluhatu ta cewa gimbiya “Ranki ya dade kin ga abin da nake sanar da ke tun ba yau ba ko. To ya kama ta a ce mun sanarwa da sarki wannan muzgunawar da suke yi mi ki domin abin a gaskiya ya yi yawa. Saboda haka ranki ya dade ni fa sai dai ki yi hakuri da ni domin ko za su kashe ni sai na sanarwa sarki irin halin da ki ke ciki a gidan nan na muzantawa. Gariyatu ta yi murmushi, sannan ta dafa kafadar Shaluhatu da yake tana zaune a kusa da ita ne da jaririn Gariyatu a hannunta ta ce mata. “Haba abokiyar shawarara nawa ma duniyar take me ya sa ba za ki kasance mai hakuri da dukkan al’amuranki ba musamman da ki ke son musulunta kamar yadda ni ma nake da niyar hakan a zuciyata. Kin riga kin san hakuri abu ne mai girma musamman ga addinin da muke so mu koma na musulunci, saboda haka ki yi hakuri da duk abin da

16

kishiyoyin suke yi min duk kuwa da cewar na san don kina kaunata ne shi yasa ranki yake baci in kin ga ana muzguna min ko muzanta min. Gariyatu ta ci gaba. “Saboda haka don Allah ‘yar uwata ki cire wannan a ranki ki maida komai ba komai ba domin duk tsanani akwai sauki a tare da shi.” Shaluhatu ta ce, “To shi ke nan uwargidana ai ban isa na tsallake umarninki ba kuma na daina fadan wannan maganar daga yau. Bayan haka kuma ni ma zan dauki irin halin na hakuri wato irin halin mutane ma’abota addinin musulunci.” Bayan Shaluhatu ta gama yin wannan bayanin na ta sai Gariyatu ta karba. “To haka duk nake son ji daga gare ki wato ki kasance mai hakuri da kauda kai daga duk abin da aka yi mi ki na muzgunawa ko muzantawa. Sannan Gariyatu ta ci gaba. “Kuma daga yau kar ki kara kirana da ranki ya dade ko kuma ki ce uwar ďakinki. Ki rika kirana kawai da sunana Gariyatu domin kiran nawa da sunana zai sa na fi jin dadi, idan kin kira ni. Sannan kar ki manta da cewar yanzu fa keba baiwar kowa ba ce yanzu ke mace ce mai ‘yanci, kamar kowace mace mai `yanci.” “Uwar dakina ke nan ai har abada ke shugabata ce kuma ban isa na daina ambatonki a matsayin uwar dakina ba. Saboda ba a taba canjawa tuko suna har kullum ni a matsayin kuyanga nake a wajenki.” Da gimbiya Gariyatu ta ji haka daga bakin Shaluhatu sai ta yi musrmushi, sannan ta ce, “To shi ke nan tunda ki ka ce haka..” Kar masu karatu su manta duk wannan badakala da ake sha tsakanin Gariyatu da kuna kishiyoyinta ko sunan dan Gariyatun ba a yi ba har żuwa wajen bokan na su da suka yi. Duk a cikin kwanakin da suka yi ne kafin a je kwana bakwai na suna. Bayan an samu kamar kwana bakwai da haihuwar Gariyatu matar sarki Illatu ranar suna ke nan ta kcwayo. Lallai a wanann ranar kasar sarki Illatu ta cika makil da baki wanda suka zo domin radin sunan jaririn da Gariyatu ta haifa. Irin kudin da sarki Illatu ya kashe a wannan rana ta radin suna abin ba zai musaltu ba don kuwa sarki Illatu ya nunawa jama’a cewa lallai neman haihuwa, saboda wannan bajintar da ya yi ta kashe makudan kudade. Ita kuwa mai jego kayan haihuwar da ya yi mata abin sai dai wanda ya gani da idanuwansa domin abin ya wuce tunanin mai tunani. A wannan rarnar aka radawa dan sarki Illatu suna Dariya, sannan aka ci aka sha tsawon mako guda ana wannan biki na suna, sannan daga bisani aka watse a wannan biki na sunan Dariya dan gimbiya Gariyatu.

17

A can kuma bayan su yarima Irwata sun sukwani dawakansu a guje, haka uha i la fama. Sai da suka shafe tsawon kwana daya suna wannan gudun daga iuni suka shiga cikin wani daji mai ni’imomi a cikinsa. Da shigarsu wannan dajin sai Irwata ya yiwa abokan tafiyarsa umarnin su Isaya a nan. Nan take kuwa wannan runduna ta sadaukai mutum dubu goma suka tsaya a wannan wajen da aka umarce su. Bayan sun gama tsayawa sai kowa ya sauka daga kan dokinsa domin su bawa dawakansu damar yin kiwo, a wanann wajcn sahoda da akwai ciyawa mai yado. A wannan wajen suka yi sallalinsu sannan aka kafa tantuna a wannan wajen sudan huta kafin su ci gaba da tafiya. Shugaban wannan runduna ta mutum dubu mai suna Galulu ya ce. ‘Ya kai shugabana ni kuma sai nake ganin kamar bai kama ta a ce tun yanzu mun fara hutawa ba in muka yi la’akari da doguwar tafiyar da take gabanmu wanda yanzu ma muka fära ta. Ga kuma hadarirrikan da ke kan hanyar tafiyar ta mu, tunda mun yi sallah, kawai mu ci gaba da yin tafiya.” Da Irwata ya ji wannan furicin daga bakin Galulu sai ya yii dariya, sannan ya dafa kafadar Galulu ya ce, “Abin da ka fada haka yake gaskiya ne kuma maganarka tana kan hanya, To amma kar ka manta da cewa mu fa “yan Adam nc kuma jiki ne da jini a gare mu sannan su kansu abubuwan da muke kan su abubuwa ne masu rai, sannan masu bukatar hutu kuma suma suna da bukatar abinci tamkar yanda mu ma mukc da bukata.” Yarima Irwata ya ci gaba. “To in ka yi la’akari da haka za ka ga ai ya zama dole a gare mu mu rika samun wajc muna hutawa sai dai kawai kar muna dogon hutu gudun tsawaitar lokaci a gare mu na zuwa kauyen Rijau. Sannan mu wuce mu tafi ga dajin Rukuki, zuwa neman ruwan albarka.” Shugaban rundunar Galulu ya ce, “Haka nc ya shugabana duk abu mai rai kan yana bukatar hutu a gare shi, sai dai in ko ba mai rai ba ne kamar yanda ka 64 ce. Yana gama fadar haka sai ya cewa mutanen cikin wannan rundunar, “Ku yi sauri ku yi aikin da shugaba Irwata ya sa mu domin ba mu da dogon lokaci a gare mu. Karamin lokaci muke da shi a yanzu. Har Galulu ya yunkura za a fara wannana aikin da shi na kafa tantuna, amma sai Irwata ya hana shi ya ja shi suka tafi wani gefe suka samu inuwa suka zauna a gindinta. Da suka samu kamar mintina uku da zama babu wanda ya ce kala a cikinsu can sai Galulu ya ce, “Ya shugabana ni kuna ina jin wannan tafiya da mukc yi ta zuwa dajin Rukuki debo ruwan albarka domin in ba wani ikon

18

Ubangiji ba duk sai mun halaka a cikin wannan dajin saboda hadarin da ke tattare da shi. Saboda tarihi ma ya nuna niutum daya ne ya taba shiga wannan dajin ya fito a raye, amma kuma da munanan raunika wanda kuma ma suka zama sanadiyar barinsa duniya.” Da Irwata ya ji wannan maganar daga bakin Galulu sai ya dan yi murmushi, kadan sannan ya ce, “Lallai maganarka haka take shiga wannan masifaffan dajin sai an yi shiri na gaske. Koda yake mu ma din ai a shirye mukc domin addu’ar ta gama ratsa jkinmu sannan bakin mu ma a koda yaushe furtata yake yi don ta daďe da zama a kan harshenmu ba ma jin komai a tarc da shi Irwata ya ci gaba. “Kuma wallahi tallahi na rantse da girman Ubangijinmu Allah zan iya yin komai don ganin masoyiyata Shalalatu ta warke daga wannan makantar a shirye nake wajnc bin duk hanyoyin da addinin mu ya tsara ganin na raba ta da wnnan lalura da ciwon ido wanda har ya zama sanadiyar makantar ta daina gani. Irwatan sannan ya dora da cewa. “Na rantse maka da girmkan Allah Galulu koda maganin da Shalalatu za ta yi amfani da shi ta samu lafiya a karkashin kasa ta bakwai yake to sai na je na nemo shi na ba ta ta yi amfani da shi don ta warkc. Kuma ma abin da ya sa tun farko ban taho wannan ruwan albarka ba da ko kaďan ban san da dajin nan ba sai a kwanakin nan limanya sanar da ni. Kuma ya ce ya boye min ne saboda ya san halina a kan taurin kai matukar ya sanar da ni da wuri to da duk wahalar wajen a lokacin sai na je na nemo wannan ruwan na àlbarka. Kuma ni wallahi har ga Allah na so a ce ni daya aka bari na taho ba tare da ku ba domin ko kadan ba na so a ce a sanadiyata an yi. asarar rayuka domin in har hakan ta faru sai na ga kamar ni na kashe mai wannan ran kuma na riga na san babu dama mu shiga wannan dajin mu fito ba a yi asarar rayuka ba. In ma ba mu mutu gaba ki daya ba ke nan. Sai dai tunda mun dogara ga Allah to da yardarsa kuwa za mu samu nasara. “To shi ke nan shugabana Ubangiji ya ba mu nasara.” To haka dai suka dinga hira har aka gama wannan tantaunan sannan suka shishshiga aka bar wasu mutane kadan a matsyin masu gadi. Tantin da yarima Irwta ya shiga shi ne wanda shugaban wannan rundunar yake ciki wato Galulu domin su su biyu ne a cikin wannan tantin. A wannan lokacin duk mutanen da ke wannan rundunar kowa ya fito da guzirinsa ya fara ci. Can da tsakiyar dare sai su yarima suka ji hayaniya da hargowa ta karade, wannan sansanin na su. Nan take yarima Irwata da Galulu suka yi saurin fitowa daga cikin wannan tantin dan ganin abin da yake faruwa.

19

Wani abin mamaki , suna fitowa kawai sai suka ga wani jibgewgen zaki da matarsa zakanya . Wadannan halittu guda biyu suna la yin barna wato suna la kashe bayin Allah wato jama’ar rundunarsu . Da Irwata da Galulu suka ga haka kawai sai suka koma gefe suka zubawa wadannan sadaukai ido domin su ga yanda za su kare da wannan zaki da kuma matarsa zakanya . Sun yi haka ne don su jarraba sadaukansu . Shi dai wannan zakin girmansa ya kai girma domin tsabar kibarsa da kyar yake tafiya , sannan ga shi da dogayen farratukan kafafuwa . Ita ma zakanyar kamar mijinta wato ita ma murgujejiya CC Kai ta rika domin saboda girman wadannan halittu – guda biyun koda kuka suka yi da gumani sai ka ji dajin ya yi amsa amo da kuwwa , ganyayyaykın bishiyoyi su ta zubowa Kasa . Ai kafin tsawon wani lokaci zakin nan tare da wannan matar tasa sun yiwa wadannan sadaukai mutum dubu goma muguwar barna domin sun kai mutum dari biyar da ‘ yan kai sannan kuma sun yiwa wajen mutane dari biyar mugayen raunika Amma saboda nacin wadannan halittu sun ki mutuwa duk da haka ma sai wani kokari suke dadawa da kuma kara kaimi don ganin cewa sun halaka wannan sadaukan rundunar . Da Irwata da Galulu suka ga irin wannan barnanr da wadannan halittu guda biyu suke yi musu sai suka dakawa sadaukan tsawa na nuni da cewar su gama da su da wuri . Ai kuwa sadaukan suna jin wannan tsawar sai ya zamana kamar tunatar da su aka yi abin da suka manta . Nan take suka yunkuro gaba ki Layansu suka yiwa wannan zakin da zakanyar kawanya . Nan da nan suka yi musu rubdugu cikin ikon Ubangiji kuma zakin da zakanyar suka zama gawa . Bayan sun kara kashe wasu dimbin sadaukan sai a yanzu ne fadan ya kare wadan da suka ji ciwo daga cikin mutanen rundunar nan suka zube suna haki . Sahi kuwa shugaban ya daka musu tsawa ya ce , “ Lallai a yi gaggawa a saka magani a jikin wadan nan sadaukan da suka ji raunika . Ba tare kuwa da hata lokaci ba sadaukai suka yi saurin suka dauko magani suka hada , sannan suka shiga shafawa masu raunikan a jikin ciwukan da ke tare da su Da aka gama shashshafa musu maganin sai aka shiga da su ciki aka kwantar da su sannan aka ci gaba da junvarsu wanda suka mutu kuma aka binne su : Bayan Irwata da shugaban sadaukai Galulu sun idar da sallah , sai Irwata ya dubi Galulu ya ce masa . “ Amma lamarin wadanan halittu ya ban mamaki domin ko kadan ban taba zaton a cikin wannan dajin mai ni ima za a samu kayan daji ba musamman da na ga ba mu dade da barin yakin kasar mu ba .

20

Da Galulu ya ji haka sai ya ce , ” Ni kaina abin ya ba ni mamaki , to amma abın nake rato a riciyata su wadannan halittu guda bivu mace da namiji wato zaki da malarsa zakanya duk yadda aka yi ruwa suka yi wucewa ta kusa da wannan shemar ta mu ko kuma suna jin yunwa ng suka hakkewa jama’armu . Amma dai yanzu bani na kira daya daga cikinsu na lambaye shi abin da ya faru . Da Galulu ya gama facin haka sai ya kira daya daga cikin jama’arsu ya lambaye shi yadda wannan abin ya faru . Wannan sadaukin ya ce , “ Mu dai muna tsaye muna gadi ne kawai sai muka hango abubuwa guda biyu suna tahowa , har ma sai muka zata ko wasu ne daga cikin dawakanmu suka iyo nan bangaren na mu . Sai da suka zo kusa da mu muka gane ha haka abin yake ba . Sai muka ga ashe zaki ne da kuma zakanya Suna zuwa kuwa sai suka iyo kanmu da nufin murkushe mu muma muka tasar musu da nufin hallaka su . Suma da suka ga haka sai suka dada kaimi da nufin su ga bayanmu . To da haka dai muke ta gabzawa da su . To ka san lamari na manyan dawa , sai a hankali domin karfin mu da zaki akwai banbanci , sosai kuma ya shi , da matarsa wato zakanya , amma fa duk da haka wallahi sadaukanmu sun yi kokari domin ka ga yanda suka rika shiga gaban zakunan babu Isoro a zukatansu duk kuwa da cewa ba karſinsu daya da da rakunan . ” . . Shugaban sadaukai Galulu ya ce , “ Haka ne kan abin da ka fada lallai sadaukanmu sun yı kokari domin fada da zaki da kuma zakanya sai a hankali Sannan yana gama fadin haka sai ya juya ya cewa Irwaia . ” Ya shugabana muna ta magana amma ba ka cc komai ba a kai . Irwata ya ce , “ Ai duk ina jin abin da ku ke fada , kuma ni ma na yaba da kokarin da sadaukanmu suka yi . To Allah dai ya raba mu da irin wannan bala’in wanda za a yi asarar rayuka bila’adadin . ‘ Suka ce , ” Ameen . Bayan an samu tsawon ‘ yan kwanaki da yin wannan gumurzun tsakanin wadannan rundunar da zaki , lokacin da jama’ar rundunar suka ji rauni sun warke garau . Sai shugaban rundunar wato Galulu ya ce da wadannan sadaukan na sa kowa gobe ya shirya domin da yaddar Allah a gobe muke son ci gaba da tafiya zuwa kauyen Rijau , wajen sarkinsu I arasu . Ina fatar hakan ya yi ya shugabanmu ? ” Irwata yana murmushi ya ce , “ Haka ya yi shugaban sadaukai dama ni ma ina so na sanar da kai zancen taſiyar sai kuma Allah ya sa ka riga ni fadan zancen ta fiyar ga sadaukanmu . ” Tun a wannan ranar sadaukai suka fara shiri kafin gari ya waye su yi haramar tafiya , Kashegari bayan sun yi sallar asuba , a nan yarıma Irwata ya

21

fara musu addu o’i da yake shi ya ja su sallar a kan Allah ya ba su nasara a kan ruwan albarha , wato dajın Rukuki . wannan alaman da suka sa a gaba na zuwa wannan dajin da za su je nemo Bayan duk sun gama abın da za su yi sai suka daurawa dawakansu surada , kan dokinsa . sannan suma da suka gama kintsawa sai kowanne daga cikinsu ya haye bisa A wannan lokacin suma su yarima Irwata da shugaban rundunar wato Galulu suka hau nasu dau akan sannan suka shiga gaba , rundunar su kuma ta mara musu baya Haka dai a wannan lokacin sun koma su dari biyar . Mutun dan biyar duk sun hallaka a sanadiyar fadan su da zakin da kuma matarsa zakanya . A can ma suka binne waďan da suka mutu . Bayan sun samu kwana da kwanaki suna tafiya a cikin wannan dajin in banda sallah da cin abinci babu abin da ke tsaida su . Haka dai suka dinga tafiya a kan dawakansu tsawon satittika har wata rana suna tafiya suka shiga wani daji mai yawan duhuwowi da kuma karancin bishiyoyin ‘ ya’yan itatuwa . Suna zuwa wannan dajin bayan da suka je tsakiyarsa sai suka rika jin hayaniya da kuka inn na kamuka . A wannan lokacin shugaban sadaukan wato Galulu ya umarci wannan rundunar ta sa da su dakata domin zuwa gano abin da ke faruwa a wannan wajen . Bayan sun gama Isayawa a wannan dajin sai yarima Irwata ya ce da Galulu hayaniyar me nake ji ke nan ? ” Galulu ya ce , ” Ai ni ma ya shugabana abin da nake ta tunani ke nan amma za mu aika wasu daga cikin rundunar mu yanzu su je su gano ko wadanna halittu ne masu kukan nan . Yana gama fadin haka sai ya ware mutane ishirin daga cikin wannan runduar ta su ya ce musu . ” Ku je ku gano mana abin da ke faruwa , sannan ku duba mana su waye masu kukan karnuka . ‘ Nan take sadaukai ishirin suka bazama neman in da wannan hayaniya take da kuma kukan karnukan da suke jiyowa . Wadannan sadaukai ashirin suka nitsa suka yi cikin wannan daj : n suka dinga tafiya har suka tarar da wadannan abubuwan da suke wannan hayaniya . Wato wasu irin halittu ne na Ubangiji wanda halittarsu ta shabanban da ta ‘ yan adam . Su dai halittun jikinsu nomal ne irin na dan adam , sai dai kansu irin na karnuka ne sannan kuma suna da jela . Bayan haka hannayensu kuma irin hannayen bururruka ne . Sannan kuma akwai zako – zako faratuna a hannayensu . Sannan wadannan halittun jifga – jifya ne masu matukar gimma . Don a takaice kowanne daga cikin wadannan halittu girmansa ya yi girman giwa , sau uku , kuma duk halittarsu daya maza da matansu .

22

Kallon wađannan halittun kawar ya ishi mutum Isoro bare kuma faca da su . Su dai wadannan halittu sun kai su dubu ishirin maza da matansu yara da manyansu . Sannan kuma suna magana . Wadannan sadaukai suka buya a cikin wala duhuwa domin jin maganar da wadannan halittu suke tallaunawa , saboda sun ga wani wanda ya fi su duk girma ya tara su a waje daya yana fada musu wata magana wanda ga alama shi ne shugabansu . Da wadannan sadaukai suka kasa kunne , sai suka ji wannan wanda suke tsammanin shi ne sarkin wannnan halittun ya ci gaba da cewa . “ To kamar yanda na faţa muku rabon da mu ga bil’adama ya shigo , wannan dajin hai mun manta shekarun ko nawa nc . Saboda haka wannan rana ta kasance ranar farin ciki a gare mu da kuma murnar da muka daļe ba mu yi ta ba ta samun naman bil’adama Bayan tsawon lokacin da muka dauka rabon mu da cin naman dan adam . Ya ci gaba da cewa “ Yanzu abin da za a yi za mu je musu no ba gaba dayan mu ba . Sai mu tura rabin mu su je su yakc su kuma duk wanda muka kashe ba za mu ci namansa danye ba za mu ajiyc gawarwakinsu ne har sai mun gama yakin gaba daya . In ya so sai mu zo mu yi farfesunsu mu cinye . Nan take sauran suka yı ihu da haushi , iriin na kare . Sannan a wannan lokacin wannan shugaba na halittun ya ba su umamin cewa kowa ya fidda makamansa domin zuwa yakar wannan runduna ta bil’adama . Ai kuwa nan da nan wadannan halittu suka rika fitowa da wasu irin muggan makamai wanda su kansu wadannan sadaukai da aka tura su yi Icken asiri ba su taba ganin irin wa’yannan makamai ba sai a wajen wadannan halittu . Da suka ga haka sai nan da nan suka fita daga cikin wannan duhuwa su ka yi saurin komawa ga rundunarsu . Da suka je suka labartawa yarima Irwata da Galulu labarin wadannan halittu da suka gano da kuma irin makaman da suke tare da su . Sannan da zantuttun da suka ji sun tattauna a kan zuwa yakarsu . Masu karatu a dai – dai nan ne zan tsaya da wannan labarin – sai mun hadu a TARTSATSIN WUTA littafi na 3 da yardar Allah . Ni ne na ku YAKUBU YAFSON MATSANGO AZARE

Wannan Shine karshen Littafi Na biyu , mu hadu A Littafi Na Uku

Karanta Littafi Na 3 Anan 👉 Tartsatshin Wuta – Littafi Na 3 Hausa Novels

— kuci gaba da bibiyar mu domin samun wasu littafan hausa Na soyayya dana Yaki A Rubuce Acikin wannan shafin Na ArewaTrending.com —

Leave a Reply