Labaran Siyasa

APC Ta dawo da karfin Ta Cewar shugaba Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce jam’iyyar APC mai mulki ta farfado da karfinta gabanin gudanar da babban taronta na kasa da kuma manyan zabukan da ke tafe.

Shugaban ya bayyana hakan ne a wata ganawa da mambobin kwamitin riko na shugabancin jam’iyyar karkashin jagorancin Gwamna Mai Mala Buni na Yobe a Abuja ranar Juma’a. 

Shugaban ya ce an sake bunƙasa jam’iyyar ne ta hanyar sake tsarawa da sasanta mambobinta a ko ina, yana mai cewa “sakamakon haka ne jam’iyyar ta farfado”.

Ya kuma ba su tabbacin ci gaba da samun goyon bayansa, da ma na sauran manyan jagororin jam’iyyar a dukkan sassan ƙasar.

—- kuci gaba da bibiyar shafin ArewaTrending.com domin samun ingantattun labaran duniya —-

Leave a Reply