Labaran Duniya

Abin Tausayi – hoton shagon matashin da ya rasa Dukiyar sa Sanadiyar gobara a kasuwar Sokoto

Wannan matashi yana daya daga cikin mutane da suka rasa Dukiyarsu a mummunar Gobarar da akayi a makonnan a babbar kasuwar sokoto.

Wannan matashi dai ya tsaya ne a bakin shagonsa yana Alhini da irin asarar da ya yi a wannan gobara.

Matashin wanda aka tabbatar da cewa shagonsa makil yake da kaya wadanda suka hada da shaddodi, Atamfa, Yadudduka da sauran abubuwa bai fita da komai ba illa Rayuwar sa.

Ubangiji Allah ya mayar masa da alkhairi da sauran yan kasar mu.

Leave a Reply